Almudahana: EFCC ta ƙwato sarƙoƙi na bilyan N14.4 a hannun Diezani

Daga UMAR M. GOMBE

Shugaban Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziki Zagon Ƙasa da Zambar Kuɗaɗe (EFCC), Abdulrasheed Bawa, ya bada bayanin cewa kimar kayan kwalliyar da aka ƙwato daga hannun tsohuwar Ministar Makamashin Fetur, Diezani Alison-Madueke, ya kai Naira bilyan N14.4.

Shugaban na EFCC ya bayyana hakan ne a Juma’ar da ta gabata a lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin Majalisar Wakilai mai bincike kan kayayyakin sata da aka ƙwato, in ji tashar Channels.

Bawa ya ce, “Kayan kwalliyar da aka ƙwato a hannun tsohuwar ministar, tsadarsu ya kai Naira biliyan N14.4 kamar yadda hukumomi suka bayyana bayan da suka duba kayan.”

Haka nan, ya ce gidajen da aka ƙwato daga hannun Diezani kimarsu ta kai Dala milyan $80, tare da cewa duka kadarorin suna nan ƙarƙashin kulawar EFCC ba a sayar da su ba.

Kwamitin majalisar na bincike ne tare da tattara bayanan adadin dukiyoyin da hukumomin gwamnati suka ƙwato daga hannun waɗanda suka wawushe dukiyar gwamnati tun daga 2002 zuwa 2020.

Idan dai ba a manta ba, a Satumban 2019 wata Babbar Kotu a Legas ta bai wa gwamnatin tarayya damar ƙwato sarƙoƙin. Inda Mai Shari’a Nicholas Oweibo ya yanke hukuncin cewa tsohuwar ministar ta gaza bada hujjar da za ta hana a ƙwace sarƙoƙin a miƙa wa gwamnatin Nijeriya.

A cikin takardar da ya gabatar wa kotu don samun zarafin ƙwato sarƙoƙin, lauyan EFCC, Rotimi Oyedepo, ya shaida wa alƙalin cewa kayayyakin sun haɗa da agogunan hannu, saƙoƙin wuya, awarwaro, wayar salulu da aka ƙera ta da zinari da dai sauransu.

Ko a farkon wannan shekara, EFCC ta miƙa ɗaya daga cikin gidajen da aka ƙwato daga hannun tsohuwar ministar ga gwamnatin Legas don a yi amfani da shi a matsayin wajen killace mutanen da suka kamu da cutar Korona.