Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
An fara samun cikakkun bayanai game da wasu daga cikin jami’an rundunar soji da ake tsare da su bisa zargin shirin juyin mulki a Nijeriya.
Majiyoyi sun bayyana cewa jami’an da ake tsare da su sun haɗa da Birgediya Janar ɗaya, Kanal ɗaya, Lieutenant Konel huɗu, Manjo biyar, Kyaftin biyu, da Laftanal ɗaya.
Sauran biyun sun haɗa da Lieutenant Commander daga rundunar ruwa da kuma Sƙuadron Leader daga rundunar sojin sama — duk daidai da matsayin manjo a rundunar sojin ƙasa.
ƙarin bayani daga majiyoyi ya nuna cewa 12 daga cikin jami’an sojin ƙasa 14 suna cikin Infantry Corps — ɓangaren yaƙi na sojojin ƙasa. ɗaya daga cikin jami’an yana cikin Signals Corps (sashen sadarwa na soja), yayin da ɗaya kuma ke cikin Ordnance Corps (sashen da ke kula da makamai, harsasai da kayan aiki).
Yawancin waɗanda ake tsare da su ‘yan waɗanda suka kammala karatunsu a NDA ne tsakanin 2004-2008, wato kwas na 56.
A farkon waɗanda aka kama akwai lieutenant colonel huɗu da manjo biyu.
Sauran jami’an sun fito daga ɗalibai na 44th, 47th, 59th, da 60th da kuma masu gajerun horaswa, Short Serɓice Courses 38 da 43.
Ba a tabbatar da kwas ɗin da wasu jami’an biyu suka yi ba, haka ma jami’an ruwa da na sama.
Majiyoyi sun ƙara da cewa 15 daga cikin jami’an 16 sun fito ne daga yankin Arewa ta Tsakiya, Arewa maso Gabas, da Arewa maso Yamma, yayin da ɗaya kaɗai daga yankin Kudu maso Yamma ne.
Majiyoyi masu tushe sun bayyana cewa wanda ake zargi da shirin juyin mulkin sun shirya kashe Shugaba Bola Tinubu, Mataimakinsa Kashim Shettima, Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, da Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas, da wasu manyan jami’ai.
Rundunar soji ta ƙi tabbatarwa ko karyata zargin, sai dai ta bayyana cewa binciken da take yi “hanya ce ta cikin gida don tabbatar da ladabi da ƙwarewa a cikin runduna.”
