Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya ce gwamnatin tarayya tana tabbatar da ‘yancin addini ga kowa tare da kare ‘yan ƙasa ba tare da la’akari da addininsu ba.
Da yake magana a CNN a daren Talata, Idris ya ƙaryata zargin wasu jami’an Amurka da ke cewa ‘yan ta’adda a Nijeriya suna kai hare-hare ne kan Kiristoci kawai.
Ya bayyana wannan iƙirari a matsayin rashin fahimtar gaskiyar yanayin tsaron ƙasar.
A cewar ministan, masu yada irin waɗannan bayanai suna taimaka wa masu tada rikici da ke ƙoƙarin haifar da rikicin addini a Nijeriya. Ya ce, “Miyagun suna kai hari ga Kiristoci da Musulmai baki ɗaya.”
Idris ya jaddada cewa Nijeriya ƙasa ce mai juriya da fahimtar juna, inda kundin tsarin mulki ke ba da cikakken ‘yancin yin addini.
Ya ce ba daidai ba ne a ce ƙasar ba ta yarda da ‘yancin addini ko cewa babu aminci a cikinta.
Ya kuma bayyana cewa gwamnatin Tinubu na ɗaukar matakai na soja da na lumana don tabbatar da tsaro da zaman lafiya, tare da ƙara kayan aiki da sauye-sauye a shugabannin rundunonin tsaro.
Ministan ya kammala da cewa Nijeriya tana ci gaba da magance matsalolin tsaro da suka addabi ƙasar tun daga shekarar 2009, tare da tabbatar da cewa kowa zai rayu cikin tsaro da kwanciyar hankali.
