CBN ya kashe Dala biliyan 1.25 duk da samuwar man matatar Dangote

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya saki Dala Biliyan 1.259 ga ‘yan kasuwa masu shigo da man fetur da sauran kayayyakin mai tsakanin watan Janairu zuwa Maris 2025, bisa sabbin bayanan gwamnati.

Rahotanni sun nuna cewa wannan mataki na zuwa ne duk da cece-kuce kan ci gaba da dogaro da shigo da man fetur daga ƙasashen ƙetare, duk kuwa da fara sarrafa mai a matakin kasuwanci daga matatar Dangote.

Sabbin bayanai daga Hukumar Kula da Haƙowa sa Tace Man Fetur (NMDPRA) sun bayyana cewa sama da kashi 69 na lita biliyan 21 da aka ci gaba da amfani da su a faɗin ƙasa daga watan Agusta 2024 zuwa farkon watan Oktoba 2025 an shigo da su ne daga ƙasashen waje – duk kuwa da iƙirarin mamatar Dangote cewa tana da isasshen ƙarfin samarwa don biyan buƙatun cikin gida har ma da fitarwa.

A cikin watanni uku na farko na 2025 kaɗai, ‘yan kasuwa sun shigo da lita biliyan 2.28 na man fetur, wanda ya zama mafi ƙaranci daga cikin adadin shigo da mai a kowace shekara a baya-bayan nan. Masana sun bayyana cewa wannan na nuna raguwar dogaro da waje, amma har yanzu shigo da mai na ci gaba da daɗa tasiri.

Bayanin yawan kuɗin da CBN ya saki don shigo da mai: Janairu dala miliyan 457.83 kashi 36.2%, Fabrairu dala miliyan 283.54 kashi 22.5%. Maris Dala miliyan 517.55 kaahi 41.3%.

Haka kuma, bayanan NMDPRA sun nuna cewa: lita miliyan 724.5 aka shigo da su a Janairu, miliyan 760 a Fabrairu, sannan miliyan 803.7 a Maris.

Haɓakar shigo da mai da kuɗin da aka saki a watan Maris na nuna ƙara tsananta gasa tsakanin matatar Dangote da ‘yan kasuwa masu dogaro da man waje.

Yanzu haka, farashi ya zama ginshiƙin da ke tantance inda ‘yan kasuwa za su sayi man fetur.

Mai magana da yawun ƙungiyar ‘Yan Kasuwar Mai ta Nijeriya (IPMAN), Chinedu Ukadike, ya tabbatar da cewa farashi ne kaɗai ke ƙayyade inda za a samo man fetur.

“A harkar nan, farashi shi ne komai,” inji shi. “Idan man da aka shigo da shi ya fi arha, ‘yan kasuwa za su saya. Idan Dangote ya sayar da ƙasa da farashin.”

Ya ƙara da cewa, hauhawar farashin ɗanyen mai a duniya, canjin kuɗin waje, da manufofin haraji na gwamnati suna taka rawa wajen bambancin farashi tsakanin man da aka sarrafa a cikin gida da wanda aka shigo da shi.

A gefe guda, ƙungiyar Manyan Masu Sarrafa Makamashi (MEMAN) a cikin rahotonta na Energy Bulletin ta bayyana raguwar farashin  fetur ɗin da ake shigowa da shi, wanda yanzu yake kimanin N805.46 a kowace lita bisa sabbin farashin kasuwa. Wannan raguwar ta samo asali ne daga faɗuwar farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya da kuma daidaitawar canjin kuɗin waje.

Masana na ganin cewa har sai matatun cikin gida sun kai matakin cikakken aiki, ’yan kasuwa za su iya tsayar da ra’ayi kan sayen man cikin gida da na waje, gwargwadon inda farashi ya fi araha.

By ukarofi