Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Majalisar Dokokin Nijeriya ta fara nazari kan muhimman sauye-sauyen Kundin Tsarin Mulki da ka iya haifar da ƙirƙirar sabbin jihohi 55 da kuma ƙananan hukumomi 278 a faɗin aasar.Rahotanni sun bayyana cewa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin (APC, Kano Ta Arewa), ne ya bayyana hakan a wani taron bita na haɗin gwiwa tsakanin majalisar dattawa da ta wakilai kan sake duba Kundin Tsarin Mulki da aka gudanar a Legas na tsawon kwana biyu.
A cewar mai magana da yawunsa, Ismail Mudashir, Sanata Barau ya sake jaddada cewa majalisar ta ƙuduri aniyar kawo gyare-gyare masu maida hankali kan buƙatun jama’a tare da tabbatar da cewa an miƙa kashi na farko na sauye-sauyen kundin tsarin mulki zuwa majalisun dokoki na jihohi kafin ƙarshen wannan shekara.
“Mun shafe kusan shekaru biyu muna aiwatar da wannan tsari — muna tattaunawa da al’ummomi, ƙungiyoyin farar hula, hukumomi, da ƙungiyoyin ƙasa domin tattara ra’ayoyi da shawarwari. A yau muna da abubuwa 69 da suka haɗa da buaatun ƙirƙirar jihohi 55, gyaran iyaka guda biyu, da ƙirƙirar ƙananan hukumomi 278,” inji shi.
Ya ƙara da cewa, ‘yan majalisa suna da alhakin tattauna da warware waɗannan shawarwarin kafin gabatar da rahoton su ga zauren majalisar, yana mai nuna fatan cewa za a cimma gagarumar nasara cikin kwanaki biyu na taron.
“Ba ƙaramin aiki ba ne wanda za mu iya kammala cikin kwanaki biyu, amma ina da tabbacin za mu iya yi, musamman tunda mun yi alƙawarin mika gyaran farko kafin ƙarshen shekara,” inji Sanata Barau.
Ya buƙaci mambobin kwamitin da su guji son zuciya da rikice-rikicen siyasa, yana mai jan hankalin su da cewa wannan aikin ya shafi moriyar ƙasa gaba ɗaya, ba wani ɓangare na musamman ba.
“Muna nan a matsayin kwamitin guda ɗaya; bai kamata mu rarrabu zuwa ‘mu’ da ‘su’ ba. Dole mu yi aiki bisa moriyar ‘yan Nijeriya gaba ɗaya,” inji shi.
Ya ƙara da cewa, an shirya wannan bita ne domin samar da shawarwari da suka dace da tanadin Sashe na 9 na Kundin Tsarin Mulki, wanda ke tsara yadda ake aiwatar da gyare-gyare a tsarin mulkin ƙasa.
