Makusantar Buhari sun koma sukar sa bayan ya bar mulki – Gwamna Sule

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya ce marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya kewaye kansa da wasu ’yan siyasa masu son kai waɗanda ke yabonsa agaban idonsa a lokacin da yake mulki, amma suka koma suna suka da zargi bayan ya sauka daga mulki.

Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Asabar a birnin Abuja yayin jawabin da ya gabatar a wajen Taron Karatun Raymond Dokpesi Diamond Lecture na biyu, wanda Cibiyar Hulɗar Jama’a ta Nijeriya (NIPR) ta shirya.

A cewarsa, gogewar zama gwamna ta ba shi damar gane irin zurfin son kai da yi wa manya yabo mara gaskiya da ke cikin siyasar ƙasar.

“Da na zama gwamna, na ga abin da son kai da yi wa shugaba yabo marar gaskiya ke iya haifarwa,” inji Sule.

“Na sha ganin mutane suna gaban Shugaba Muhammadu Buhari suna cewa, ‘Kai ne mafi nagarta, babu wanda ya kai ka,’ amma da zarar ya sauka daga mulki sai su koma suna cewa, ‘Shi ne ɗaya daga cikin mafi raunin shugabannin da Nijeriya ta taɓa samu.’ Mutane ɗaya ne, amma lokuta ne daban. Wannan shi ne ainihin ma’anar son kai da yi wa shugaba yabo da ya wuce kima.”

Gwamnan, wanda ya karɓi kyautar girmamawa da lambar gwaninta ta NIPR, ya yi amfani da damar wajen tunawa da marigayi Chief Raymond Dokpesi, wanda ya bayyana a matsayin jarumi kuma mai hangen nesa wanda ya fuskanci ƙalubale wajen yaƙar tsauraran dokokin gwamnati a lokacin da kafafen yaɗa labarai suke ƙarƙashin kulawa ta soja.

Ya tuna cewa Dokpesi ne ya kafa kamfanin DAAR Communications, masu gidajen talabijin da rediyon AIT da RayPower, inda ya buɗe sabon babi a tarihin kafafen watsa labarai masu zaman kansu a Nijeriya.

“Muna nan domin tunawa da gwarzon kafafen yaɗa labarai,” inji Sule.

“Dokpesi bai taɓa jin tsoron faɗin gaskiya ga masu mulki ba, ko a lokutan da gwamnati ke da cikakken iko akan labarai.”

A nasa ɓangaren, shugaban NIPR, Dr. Ike Neliaku, ya yaba wa Gwamna Sule saboda bada fili ga cibiyar domin gina makarantar farko ta ƙasa da za ta koyar da dabarun hulɗar jama’a a matakin duniya a Jihar Nasarawa.

Ya ce, aikin ginin makarantar ya kai matakin ci gaba sosai, kuma za ta taimaka wajen samar da sabuwar ƙarni na masu fasahar sadarwa masu ɗabi’a da tunani mai zurfi a harkar shugabanci.

Neliaku ya bayyana wannan jami’a mai zuwa a matsayin “Cibiyar Ilimi ta Musamman” da za ta haɗa tsakanin tsara manufofi da isar da saƙonni ga jama’a cikin tsarin mulki.

Taron, wanda aka gudanar domin tunawa da gagarumar gudunmawar Dokpesi wajen kafa ’yancin kafafen yaɗa labarai da jawo tattaunawa kan harkokin ƙasa, ya haɗa manyan jami’an gwamnati, masana sadarwa, ’yan jarida da sauran kwararru a fannin yaɗa labarai.

By ukarofi