Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana fargaba mai tsanani bayan rahotannin da suka nuna cewa, ’yan ta’adda na Boko Haram sun fara amfani da jirage marasa matuƙi (duron) wajen kai hare-hare a yankin Arewa maso Gabas, wani sabon salo da ke nuna cewa yaƙin da ake da su ya shiga wani mataki mai hatsari.
A garin Mafa, inda ya taru da jami’an tsaro da shugabannin al’umma, Zulum ya ce, “Wannan lamari abin firgici ne. A Dikwa, an tabbatar min cewa an yi amfani da diron wajen kai hari. Ya zama dole gwamnati ta ɗauki mataki domin hana yaɗuwar amfani da diron a hannun ’yan bindiga.”
Wani rahoton da jaridar News Point ta wallafa ya bayyana cewa, wannan gargaɗi na gwamnan na zuwa ne bayan rahotannin leƙen asiri da suka nuna cewa garin Mafa — garin da Zulum ya fito – na fuskantar harin Boko Haram ko ISWAP a kowane lokaci.
Zulum ya roƙi Gwamnatin Tarayya da ta sake duba tsarin tsaron sararin samaniya da kuma tsarin kariyar ƙasa, yana mai cewa lamarin ya nuna “rami mai hazari” a tsarin tsaron Nijeriya.
Sabon salo na yaƙin Boko Haram:
Shekaru 16 kenan da Nijeriya ke fama da wannan ta’addanci, amma amfani da diron na nuna sabon salo na yaƙi mai amfani da fasahar zamani, maimakon kai da kwanton-ɓauna kamar da.
Masana harkokin tsaro sun ce wannan sauyi na iya zama mafi haɗari tun bayan 2011, lokacin da ƙasar ta shiga cikin mummunan yanayin tashin bama-bamai da aka fi saka wa a jikin mata da yara.
A ranar 21 ga Yuni 2025, wata mace ta tayar da bam a kasuwar kifi ta Konduga, kilomita 25 daga Maiduguri, inda ta halaka mutane 12 — shi ne haren bam na farko a shekarar 2025 bayan shekaru da dama da aka samu sassauci.
Sojoji da dama sun rasa rayukansu:
Bayan wannan harin, Boko Haram ta sake kai farmaki a yankin, inda sojoji 7 suka mutu, wasu kuma suka jikkata. A wani hari daban, sojoji 17 suka rasa rayukansu bayan mayaƙan sun farmaki sansanonin rundunar soji uku. A Marte, an kashe sojoji 10 kuma ‘yan ta’addan suka kwashe makamai da motocinsu.
Duk da wannan, dakarun ƙasashen yankin tafkin Chadi – ƙarƙashin MNJTF – na ci gaba da fama da ƙalubalen. Chadi ta janye dakarunta tun Janairu 2024 bayan asarar rayuka, yayin da Nijar ta bi sahu a watan Afrilu. Hakan ya bar Nijeriya da Kamaru cikin ƙuncin da ke iya ba wa Boko Haram damar sake kafa sansanoni.
Mutuwar shugaban Boko Haram ba ta kawo ƙarshen barazana ba:
A watan Agusta, hukumomin Nijar sun tabbatar da kashe shugaban Boko Haram, Bakura Doro, ta harin diron. Amma duk da hakan, hare-haren Boko Haram sun ƙaru a yankin tafkin Chadi – alamar cewa an samu sabbin shugabanni masu tsattsauran ra’ayi.
Masani Michael Nwankpa ya ce: “Bakura Doro ba ya son ya riƙa bayyana a kafafen yaɗa labarai ba, ya fi mayar da hankali kan sake gina aungiyar cikin sirri.”
Sabon barazana ga Nijeriya:
Yayin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke fama da matsalolin tsaro a arewa maso yamma, kudu maso gabas da yankin Neja-Delta, sabon barazanar Boko Haram na amfani da diron ya ƙara dagula al’amura.
Bayan harin Konduga, Tinubu ya wallafa saaon ta’aziyya a dandalin ɗ (Tsohon Twitter), yana cewa: “Ba za mu lamunci ƙoƙarin yaɗa tsoro ba. Hukumar tsaro ta shafe ragowar Boko Haram.”
Sai dai har yanzu, ƙungiyar ta nuna cewa tana da ƙarfi da dabaru na zamani.
Yaƙin bai ƙare ba – Zulum:
Gwamna Zulum ya jaddada cewa dole ne gwamnati, sojoji, da al’umma su haɗa kai wajen gano giɓin tsaro da gyarawa.
“Ina kira ga gwamnati da duka ɓangarori su tashi tsaye — domin wannan sabon salo na barazana ba na Borno kaɗai ba ne, na Nijeriya ce baki ɗaya.”
Bayan shekaru 16 da aka shafe ana yaƙi da Boko Haram, sabon salo da suka ƙaddamar yanzu — yaƙin diron da bam na fasahar zamani — na nuna cewa yaƙin Arewa maso Gabas na sake shiga sabon zango mai cike da haɗari.
