Daga AISHA ASAS
Tun bayan fitowar Jagun Jagun: The Warrior a shekarar 2023, fim ɗin ya samu karɓuwa daga masu kallon fina-finan Najeriya, musamman saboda labarinsa na yaƙi, iko da gwagwarmayar wani matashi da ya ƙalubalanci wani fitaccen shugaban mayaƙa. A yanzu kuwa, mai shirya fim ɗin, Femi Adebayo, ya sake ɗaga hankalin masu sa ido, bayan bayyana wasu daga cikin jaruman da za su fito a kashi na biyu.
Cikin sabbin fuskokin da aka bayyana akwai fitacciyar jaruma Funke Akindele da mawaƙan Fuji Wasiu Ayinde, wanda aka fi sani da Kwam 1, da Wasiu Alabi, wato Pasuma. Haka kuma, Muka Ray da Cute Abiola na cikin waɗanda za su shiga aikin. A cewar rahoton Premium Times na 16 ga Oktoba, 2026, za a haɗa waɗannan da wasu jaruman da suka taka rawa a fim ɗin farko.
Wannan haɗuwar jarumai daga sassa daban-daban na nishaɗin Najeriya na iya zama ɗaya daga cikin abubuwan da za su sa masu kallo su sa ido kan fim ɗin. Sai dai, ba sunayen da aka tattara a jerin jarumai ne kaɗai za su tabbatar da nasarar sabon fim ɗin ba; yadda aka gina labarinsa da yadda kowanne jarumi ya taka rawarsa ne za su taimaka wajen tantance yadda masu kallo za su karɓe shi.
Femi Adebayo ya bayyana cewa shirya fim ɗin ya ɗauki tsawon shekaru biyu, tare da sadaukarwa da ƙalubale a yayin gudanar da aikin. A wani rahoto da ɓoice of Nigeria ta wallafa, ya bayyana cewa ya zubar da hawaye saboda nauyin tafiyar da aikin, yana mai danganta hakan da abubuwan da ya fuskanta kafin a kammala shi.
A fim ɗin farko, labarin ya ta’allaka ne kan Ogundiji, wani jagoran yaƙi mai iko, wanda matsayinsa ya fara fuskantar barazana bayan bayyanar Gbotija, wani matashi da ke neman ɗaukar fansar mutuwar mahaifinsa. Wannan rikici tsakanin iko, buri da neman adalci ne ya gina tushen labarin farko, wanda ya samu lambobin yabo a shekarar 2024.
