Daga CMG HAUSA
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yau Jumma’a cewa, an cimma matsaya, da nasarori a wasu muhimman batutuwan da suka shafi tsaro da ci gaban duniya, a wajen taron ministocin harkokin wajen ƙasashen BRICS da aka yi ta kafar bidiyo a jiya Alhamis, matakin da ya share fage sosai a fannin siyasa, da gudanar da ganawar shugabannin ƙasashen BRICS karo na 14.
Jiya Alhamis, memban majalisar gudanawar ƙasar Sin, wanda kuma shi ne ministan harkokin wajen ƙasar Wang Yi, ya jagoranci shawarwari ta kafar bidiyo, tsakanin ministocin harkokin waje na ƙasashen BRICS, da na kasashen dake da sabbin kasuwanni, da na ƙasashe masu tasowa. Ministocin harkokin waje, ko kuma wakilansu daga ƙasashen BRICS, da na Kazakhstan, da Saudiyya, da Argentina da sauransu, sun halarci shawarwarin.
Wang Wenbin ya jaddada cewa, wannan salon haɗin-gwiwa da ake kira “BRICS+”, dandali ne da aka kafa ga ƙasashen dake da sabbin kasuwanni da kasashe masu tasowa. Ƙasar Sin na maraba da ƙarin ƙasashe su shiga ciki, don kara shimfida tafarkin demokuraɗiyya a huldodin ƙasa da ƙasa, da raya tattalin arzikin duniya don amfanin kowa da kowa, da kuma tafiyar da harkokin mulkin duniya yadda ya kamata, a wani ƙoƙari na ƙirƙiro makoma mai haske.
Mai fassara: Murtala Zhang
