Wang Wenbin: Fatanmu shi ne Amurka ta aiwatar da abubuwan da ta alƙawarta

Spread the love

Daga CMG HAUSA

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce ƙasar sa na fatan Amurka za ta inganta kawancen ta da ƙasashen dake yankin Asiya da tekun Pacifik, za ta kuma ƙara azama wajen ingiza zaman lafiya da ci gaba, maimakon rura wutar rikici, da tada zaune tsaye a yankin. Wang ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai na Juma’ar nan a birnin Beijing.

A yau Juma’a ne shugaban Amurka Joe Biden ya isa Koriya ta Kudu, inda zai gana a karon farko da sabon shugaban ƙasar Yoon Suk-yeol. Kuma tun a ranar Laraba ne, mashawarcin shugaban na Amurka ta fuskar tsaron ƙasa Jake Sullivan, ya bayyana cewa, ziyarar da shugaba Biden din zai gudanar a nahiyar Asiya, ba ta da nasaba da yin fito-na-fito da ƙasar Sin.

Game da hakan, Wang ya ce abun fatan dai shi ne Amurka ta aiwatar da abubuwan da ta alƙawarta, ta kuma yi aiki tare da sauran ƙasashen yankin tekun Indiya da Pacific da Asiya, don yayata dunƙulewa da haɗin gwiwa, maimakon kitsa matakan rarrabuwar kawuna da fito na fito.

Game da batun tsarin nan na ingiza tattalin arzikin yankin, wadda Amurka ta tsara ƙaddamarwa yayin ziyarar ta Mr. Biden, Wang ya ce Sin na da ra’ayin cewa, ya kamata duk wani tsari na shiyya ya dace da zamanin da ake ciki, ta yadda hakan zai haifar da yanayin zaman lafiya da ci gaba, kana ya kamata tsarin ya ingiza amincewa da juna, da haɗin gwiwa tsakanin kasashen shiyyar, ya kuma ƙunshi kowa da kowa ba tare da wariya ba. Kaza lika bai dace a yi amfani da shi wajen muzgunawa wani ɓangare ba.

Fassarawa: Saminu

By Editor