Daga BASHIR ISAH
An kama wani mai suna Maiwada Dakata bisa zarginsa da hannu a garkuwar da aka yi da mahaifiyar dan takarar Sanatan Kano, A.A Zaura.
Mai magana da yawun Zaura, Al-Amin Ciroma, shi ne ya bayyana haka a shafinsa na facebook a ranar Laraba.
Ciroma ya ce Maiwada Dakata amini ne mai kama da dan’uwa ga A.A Zaura saboda yadda suka taso tare, amma ana zarginsa da jagorancin garkuwar da aka yi da Hajiya Laure Mai Kunu, mahaifiyar A.A Zaura.
“Jami’an tsaro sun damke wanda ake zargin ne otel a lokacin da yake hutawa tare da budurwarsa yayin da yake jiran kuɗin fansa, a zatonsa ya gama zama attajiri,” inji Ciroma.
Da safiyar Litinin da ta gabata aka yi garkuwa da Hajiya Laure a gidanta da ke garin Zaura cikin karamar hukumar Ungogo a Jihar Kano, inda kuma aka sako a ranar Talata.
