Daga BASHIR ISAH
Tsohon Gwamanan Jihar Legas kuma jigo a Jam’iyyar APC, Cif Asiwaju Bola Aahmed Tinubu, ya zama dan takarar da zai nemi shugabancin Najeriya karkashin Jam’iyyar APC a babban zaben 2023.
Tinubu ya taki wannan nasarar ce bayan kammala zaben fidda gwanin da Jam’iyyar APC ta gudanar a Abuja.
Jigon jami’yyar ya yi nasarar a kan abokan hamayyarsa ne bayan da ya yi musu fintinkau da kuri’ 1,271.
Tun farko, ‘yan takara 23 ne aka tantance don shiga zaben fidda gwani, amma daga bisani an samu wadanda suka janye don goya wa sauran baya.
Yayin zaben fidda gwanin, Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya samu kuri’u 235, Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya samu 152, Gwamna Yahaya Bello kuri’u 47, da suaransu
Da wannan, ya tabbata cewa zaben 2023, duka hankula za su karkata ne kan manyan ‘yan takarar da ake ganin su ne kan gaba, wato Tinubu na Jam’iyyar APC da kuma Atiku na babbar jam’iyyar hamayya.
