Daga BASHIR ISAH
Mutum biyu aka ruwaito sun riga mu gidan gaskiya a safiyar Laraba sakamakon gobarar da ta tashi a wani gidan mai da ke kusa da Alaoji a hanyar Ikot-Ekpene, cikin ƙaramar hukumar Obingwa, Jihar Abia.
Kwamandan Hukumar Kwana-kwana na Shiyyar Aba, Mr Belenta Belenta, ya tabbatar da faruwan hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a ranar Laraba.
Belenta ya ce, yana zargin waɗanda lamarin ya rutsa da su suna ƙoƙari satar mai ne wanda hakan ya yi sanadiyar zubewar fetur ɗin da ya yi sanadin ta da gobarar.
Ya ci gaba da cewa, gobarar ta laƙume wasu manyan motoci guda biyar da ke ajiye kusa da gidan man.
Ya ƙara da cewa, bayan da labarin gobarar ya isa gare su, sun tura jami’ansa sun kashe gobarar, kana ‘yan sanda sun bayyana a wurin inda suka kwashi gawarwakin mutum biyun da suka mutu nan take zuwa ɗakin ajiyar gawarwaki.
Sai dai, wani ganau ya ce “Akwai tankoki guda huɗu da ke sauke mai a lokacin da lamarin ya auku.
“Mun ji cewa tartsatsin wutar lantarki da aka samu daga janaretan gidan man ne silar gobarar,” inji ganau ɗin.