NDC ta yi Allah wadai da kisan Bindin a Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Jam’iyyar National Democratic Congress (NDC), reshen Jihar Zamfara, ta yi Allah wadai da harin da aka kai a kwanan nan a garin Bindin da ke ƙaramar hukumar Maru a Jihar Zamfara, wanda ya yi sanadiyyar kashe jami’an tsaro da fararen hula da kuma ɓarnata dukiyoyi.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar, wadda sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar, Kassim Almustapha Kayatawa ya sanya wa hannu, kuma aka baiwa manema labarai a Gusau yau Laraba.

Jam’iyyar ƙarƙashin jagorancin Alhaji Surajo Garba Maikatako, ta miƙa saƙon ta’aziyya ga al’ummar Bindin, tana addu’ar Allah ya jiƙan waɗanda suka rasu kuma ya baiwa iyalansu haƙurin jure rashin”.

Sai dai jam’iyyar ta nuna takaicinta kan rashin halartar Gwamna Dauda Lawal a lokacin wannan alhini, tana zargin cewa gwamnan ya zaɓi ya bi tawagar gwamnatin tarayya don wani taro kan hada-hadar shugabanci tsakanin Najeriya da Habasha kan manufar abinci mai gina jiki a Addis Ababa maimakon ya kasance tare da al’ummarsa.

A cewar NDC, wannan mataki rashin tausayi ne kuma cin amanar al’umma ne, inda ta tunasar da cewa Gwamna Lawal ya yi alƙawari a lokacin kamfen din zaɓen 2023 cewa zai kawo ƙarshen ‘yan bindiga a Jihar Zamfara.

“Shugabanci ana bayyana shi ne da tausayi a lokacin rikici, ba da ɗaukar hoto a ƙasashen waje ba. Al’ummar Zamfara sun cancanci shugaban da ke ba da fifiko ga tsaronsu da walwalarsu fiye da komai,” in ji sanarwar.

Jam’iyyar ta ƙara yin Allah wadai da Gwamnatin Tarayya kan amincewa da shigar Gwamna Lawal cikin tawagar ta zuwa ƙasashen waje alhali jiharsa na cikin hare haren ‘yan ta’adda.

Jam’iyyar ta bayyana amincewar Gwamna Dauda Lawal yabi tawagar gwamnatin tarayya zuwa ƙasar Habasha a matsayin matakin rashin tausayi da nuna rashin sanin halin da al’umma su ke ciki a Jihar ta Zamfara.

“Matakin gwamnatin tarayya na amincewa da zuwan gwamnan, maimakon ta buƙaci ya kasance a jiharsa a lokacin rikicin tsaro, gazawa ce babba ta shugabanci ga kowane ɗan jihar Zamfara,” in ji NDC.

NDC ta bayyana cewa jami’an tsaron da suka rasa rayukansu a Bindin sun mutu a matsayin jarumai kuma sun cancanci a karrama su, ba a yi watsi da su ba.

Ta yi kira ga Gwamna Dauda Lawal da ya dawo Zamfara ya yi jawabi ga al’umma.

Jam’iyyar ta kuma buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta bayyana dalilin da ya sa ta ba da fifiko ga tafiyar ƙasashen waje fiye da rayukan ‘yan ƙasa, kuma ta yi kira da a gurfanar da waɗanda suka aikata harin a gaban shari’a.

Jam’iyyar ta kuma buƙaci al’ummar Zamfara da su ci gaba da kasancewa masu haɗin kai, kuma ta buƙaci al’ummar duniya da su kula da taɓarɓarewar yanayin tsaro a jihar.

By ukarofi

Leave a Reply