Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
‘Yan sandan sun sami nasarar daƙile kai hare hare a ƙananan hukumomin Kankia da Musawa tare da ceto mutane uku da shanu 12.
Wata sanarwa ɗauke da sa hannun jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya fitar,bayan da samun labari na ‘yan bindiga sun kai farmaki a ƙauyen Fakuwa “nan take DPO na ofishin ya tada haɗin gwiwa na ‘yan sanda da ‘yan banga suka kai ɗauki a ƙauyen”,Inji Sadiq.
Bayan ɗauki da ɗauki ba daɗi da jami’an tsaron suka fatattaki ‘yan bindigan suka tsere suna ɗauke da manyan raunuka.
Jami’an tsaron sun sami nasarar ceto mutane da dabbobin da ‘yan bindigan sukai yunƙurin sacewa.
Mutanen sun haɗa da Jamila Alti yar shekara 50 da Aisha Alti Mai shekara 15 da haihuwa da wani dattijo ɗan shekara 60 waɗanda suna cikin ƙoshin lafiya tuni aka sada su da iyalansu.
Haka Kuma a ƙaramar hukumar Musawa yan bindigan suka mamaye hanyar Kiryoyi zuwa Dangani sai dai nan take DPO na Musawa ya aike da tawagar ‘yan sanda zuwa wurin da ‘yan bindigan sukai ƙawanya “bayan ɗauki ba daɗi da ‘yan sanda sun yi nasarar fatattakar ‘yan bindigan wanda suka gudu suna ɗauke da manyan raunuka.
Sai dai ‘yan sanda sun gano gawar ɗaya daga cikin yan bindigan yana ɗauke da mummunar rauni da akai masa da adda.
DSP Abubakar Sadiq ya bayyana cewa jami’an tsaron za su cigaba da farautar ‘yan bindigan da suka tsere zuwa dazuka da nufin kamo su su fuskanci shari’a.
Kwamishinan ‘yan sanda CP Ali Fage ya yaba wa jami’an sa bisa nuna ƙwarewa da jajircewa wajen yaƙar waɗannan ‘yan ta’adda a jihar.
