Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a p
Wata mata mai suna Hauwa Umar Saulawa ta shigar da kara a babbar kotun Jihar Katsina, tana zargin cewa an take mata haƙƙoƙin ɗan Adam ta hanyar kama ta, tsare ta da kuma yi mata bulala 33 a wani lamari da ya shafi zargin yunƙurin zina.
Shari’ar mai lamba KTH/3077/2026 an shigar da ita ne a babbar kotun jihar Katsina, sashen shari’a na Katsina, inda lauyan mai ƙarar, Mujaheed Alameen na Imtiyaz Law Chambers, ya gabatar da buƙatar a madadin wadda ta shigar da ƙarar.
Waɗanda ake ƙara sun haɗa da hukumar Hisbah ta Jihar Katsina; Malam Muhammad Shitu Maslaha, tsohon mataimakin kwamandan-janar (DCG) mai kula da ayyukan hukumar; Malam Nafiu M. Akilu, OC Team Operation; Huraira Ahmad, daga tawagar ayyukan ɓangaren mata ta Hisbah; da Kabiru Mashi, wanda aka fi sani da “KB Engineer”.
A cikin takardar da aka gabatar wa kotu, Hauwa ta buƙaci kotun ta bayyana cewa kama ta da tsare ta da aka yi a ranar 21 ga Agusta 2026, wanda ta ce ya ci gaba har zuwa misalin ƙarfe 3:00 na ranar 22 ga Agusta, ya saɓa wa haƙƙin ta na samun ’yanci da kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.
Ta kuma zargi Waɗanda ake ƙara da hannu wajen yi mata bulala har sau 33, tana mai cewa lamarin ya take mata haƙƙin mutunci da aka tanada a ƙarkashin sashe na 34 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na 1999, wanda aka yi wa kwaskwarima.
Mai ƙarar ta kuma buƙaci kotu ta bayyana cewa kama ta, tsare ta, cin zarafinta da kuma yi mata bulala dangane da zargin yunƙurin zina sun saɓa wa doka tare da take mata haƙƙokinta.
Hauwa ta kuma dogara da tanade-tanaden African Charter on Human and Peoples’ Rights, inda ta ce abubuwan da take zargin waɗanda ake ƙara da aikatawa sun saɓa wa haƙƙoƙin da yarjejeniyar ta tanada.
Kamar yadda Katsina Time ta ruwaito,cikin buƙatun da ta gabatar wa kotu akwai umarnin da zai hana waɗanda ake ƙara, jami’ansu ko wakilansu sake kama ta ba bisa ƙa’ida ba, tsare ta, dukanta, yi mata barazana ko kuma cin zarafinta dangane da wannan lamari.
Ta kuma nemi kotu ta umarci waɗanda ake ƙara su biya ta Naira miliyan biyar (N5m) a matsayin diyya kan zargin take mata haƙƙi, tare da ba ta rubutacciyar takardar neman afuwa.
Haka kuma, ta nemi a biya kuɗaɗen shari’ar da kuma duk wani ƙarin umarni da kotun za ta ga ya dace.
Takardar buƙatar da aka gabatar wa kotun tana ɗauke da ranar 7 Oktoba 2026.
Zarge-zargen da ke cikin takardar ƙarar ikirari ne daga mai ƙarar da ake gabatarwa a gaban kotu. Ya zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, hukumar Hisbah ta Jihar Katsina da sauran waɗanda ake ƙara ba su fitar da martani kan zarge-zargen ba.
