Daga BASHIR ISAH
An garzaya da Sarki Salman bin Abdulaziz na Saudiyya zuwa asibitin Jidda domin ci gaba da duba lafiyarsa.
A ranar Lahadi Kamfanin Dillancin Labarai na Saudiyya ya ba da sanarwar garzayawar da aka yi da basaraken mai shekaru 86 zuwa a asibiti.
Rahoton Masarautar Saudiyya ya nuna a ranar Asabar ne Sarki Salman ya tafi Asibitin Ƙwararru na Sarki Faisal don bincika lafiyarsa.
A shekarar 2015 ne Sarki Salman bn Abdulaziz ya ɗare kujerar sarauta a matsayin sarkin Saudiyya na bakwai biyo bayan rasuwar Sarki Abdullah bin Abdulaziz.
Kafin wannan lokaci, Sarki Salman ya tafi asibiti a watan Maris da ya gabata don ganin likita
Rahotanni daga Saudiyya sun tabbatar da Masarautar Saudiyya da ma al’ummar ƙasar baki ɗaya na ci gaba da addu’ar samun lafiya ga sarkin nasu.
