Shugaba Buhari ya tafi taron Majalisar Ɗinkin Duniya

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya keta hazo zuwa Abidjan a Ƙasar Cote d’Ivoire domin halartar taron Majalisar Ɗinkin Duniya.

Taron zai maida hankali ne kan abin da ya shafi lalubo hanyoyin magance matsalolin zezayar ƙasa, fari, gushewar dazuzzuka da sauransu da kuma tasirinsu ga tattalin arzikin duniya.

Wannan shi ne karo na goma sha biyar da MƊƊ ke shirya irin wannan taro wanda zai gudana daga ranar 9 zuwa 10 na watan Mayun 2022.

Sanarwar da ta fito ta hannun Kakin Shugaban Ƙasa, Malam Garba Shehu, ta nuna babban taron zai tattauna a kan matakan da suka dace a ɗauka don tabbatar da al’ummar yau da na gobe sun ji daɗin zaman duniya.

A cewar sanarwar, “Domin cin ma manufar wannan taro akwai buƙatar haɗo kan shugabannin daga gwamnati da ɓangaren ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki daga sassan duniya domin tattauna yadda za a kare ƙasa da tattalinta.”