Akwai ƙoƙarin da muke yi na inganta tsarin makarantun tsangaya – Gwani Jibrin

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Tun bayan sake ci gaba da muhawarar da ta taso a zaurukan sada zumunta dangane da zargin da wata jarumar finafinan Hausa, Nafisatu Abdullahi ta yi game da gararambar yara ƙanana suna yawon bara a titi, babu kulawar iyaye, ‘yan Nijeriya ke ta tofa albarkacin bakinsu game da illar tura yara ƙanana almajiranci da samar da sabon tsari ga makarantun tsangaya, yadda za su dace da zamani. Shugaban Ƙungiyar Inganta Ilimin Tsangaya na ƙasa wato Tsangaya Education Development Initiative, ƙarƙashin gamayyar wasu manyan alarammomin Nijeriya, GWANI JIBRIN YAHAYA ALQASIM, ya gana da wakilin Blueprint Manhaja ABBA ABUBAKAR YAKUBU a Jos, inda suka tattauna kan irin ƙalubalen da ilimin tsangaya ke fuskanta, zargin ɓata suna da wasu ‘yan siyasa da ‘yan boko suke yi wa almajirai da kuma halin ko-in-kula da gwamnati ke nunawa ilimin tsangaya a Nijeriya. A sha karatu lafiya.

MANHAJA: Malam, ko za ka gabatar mana da kanka?
GWANI JIBRIN: (Bismala da addu’ar farawa) To, Alhamdulillahi. Ni dai kamar yadda aka sani sunana Gwani Jibrin Yahaya Alƙasim, kuma ni ne shugaban ƙungiyar alarammomi ta Tsangaya Education Development Initiative, ƙungiyar da aka kafa don kare martaba da mutuncin karatun tsangaya. Ni almajiri ne, kuma na yi karatuna a wajen malamai da gwanayen Alƙur’ani da dama, kamar irin su Gwani Muhammad da ke garin Zariya, akwai Gwani Sa’idu da ke Kaduna, sai kuma daga baya na ta fi ƙasar Borno na je neman sirrin Alƙur’ani inda na zauna a Unguwar Gwange, kafin daga bisani na koma garin Potiskum tsangayar Gwani Mai Buzu. Allah ya jikan su, Allah ya gafarta musu baki ɗaya.

Mene ne karatun tsangaya ke nufi?
Karatun tsangaya wani tsari ne na neman ilimin Alƙur’ani mai girma, ta hanyar amfani da allo, wanda ake rubuta shi da alƙalami da tawada. Iyayen yaro ne ke bayar da ɗansu ga wani malami da suka yarda da halayensa da iliminsa, domin ya ɗauke shi daga gaban iyayen sa ya kai shi wata tsangaya nesa da gari, inda babu gatansa, don ya mayar da hankali ya yi karatu ta yadda zai samu haddar Alƙur’ani. Kamar dai yadda ya ke a tsarin karatun boko, inda iyaye ke tura yaransu zuwa makarantar kwana a wani gari ko wata jiha, don su samo ilimin boko. 

Mene ne ya bambanta karatun tsangaya da zuwa bara da almajirai ke yi? 
Babu shakka karatun Alƙur’ani daban ita kuma bara daban. Kamar yadda za ka samu mabarata a titi, waɗanda idan ka bincika da kyau za ka tarar ba almajirai ba ne, babu wata makaranta da suke zuwa karatu kuma babu wani malami da suke zaune a ƙarƙashinsa. Tabbas ana samun yaran almajirai da suke zuwa barar neman abinci, ko da ya ke kuma akwai waɗanda ba sa barar. Amma yanzu masu barar su suka fi yawa, saboda mutane masu hali da su ne ya kamata su ɗauki nauyin kula da makarantun tsangaya, saboda amfana da suke yi da addu’o’i da saukar Ƙur’ani da ake yi musu, amma sai suka juya baya suka sa duniya a gaba, a ka bar malami da almajiransa babu mai kula da su. Ka ga kuwa dole yaro ya shiga barar abin da zai ci, ba lallai don yana so ba, kuma komai yawan abin da iyayensa suka haɗo shi da su. 

Malam, yaya ka ke ji irin zarge zarge da mutane ke yi na rashin dacewar yadda ake ɗauke yara masu ƙananan shekaru daga gaban iyayensu, suna shiga gari suna zama fitina ga al’umma idan sun girma, saboda rashin samun kulawar iyaye da tarbiyya? 
Wannan kuma zan kira shi da son zuciya ne kaɗa’an da kuma jahilci kan abin da karatun tsangaya ke nufi. Babu inda za ka je ka ji an ce an kama wani almajirin tsangaya da ya tashi gaban alaramma wane, yana harkar daba ko Sara Suka, ko garkuwa da mutane, ko ta’addanci. Masu irin wannan halayyar a gaban iyayen su suka girma, ba daga makarantar allo ake koyon rashin tarbiyya da ta’addanci ba, sai a rufe ido saboda qin gaskiya, a yi wa almajirai ƙazafi, don ba a son ganin su a gari suna yawo cikin tsumma. 

Akramakallahu, ko za ka gaya mana yadda aka yi ku ka kafa wannan ƙungiya ta malaman tsangaya?
To, a gaskiya mun yanke shawarar kafa wannan ƙungiya ne domin samar da haɗin kai tsakanin alarammomi masu koyar da ilimin sanin Alƙur’ani a makarantun tsangaya, da nufin samar da gyare gyare da inganta tsarin yadda ake gudanar da makarantun mu da kuma buɗe wata ƙofa da za a riƙa tattaunawa tsakanin mu da muke malaman tsangaya na ainihi da gwamnati ko hukumomi da sauran jama’a masu ƙorafe-ƙorafe kan almajirai da tsarin makarantun allo. Saboda wadansu suna yin sukar ne kawai, ba su san ainihin inda ya dace su gabatar da ƙorafin su ko shawarwarin su ba. Kuma mu da muke rayuwa a cikin wannan tsari muka san shi gaba da baya, mune ya fi dacewa mu fito mu kare mutuncinsa.

Wanne tsari ku ka yi wa wannan ƙungiya don ganin ta cimma muradin kafuwarta?
Babu shakka muna da tsare-tsare da dama da muka ɗora harsashin ƙungiyar mu a kai, kuma muna da burin ganin an kawo canje-canje na zamani da za su kawo gyara a tsarin tafiyar da makarantun tsangaya. Muna son mu gyara kan mu da kan mu. Domin ba ma jin daɗin yadda gwamnati ke kafa kwamitoci ko wata hukuma da za ta binciki tsarin makarantun tsangaya, inda sai ka ga an naɗa wani da zai jagoranci al’amarin tsangaya alhalin bai san komai a harkar karantar da almajirai ba. Maimakon a samu gyara, sai ka ga an samu varna. Ana yawan zargin makarantun mu da bazuwar yara a gari suna bara, alhalin yawancin waɗanda ake gani a tituna ba almajirai ba ne zalla, akasari mabarata ne kawai, kuma da iyayen su a gari, amma da an gansu da kwanon bara, sai a yi musu kuɗin goro, ana cewa duk almajirai ne. Sam, ba ma jin daɗin wannan, domin ni shaida ne a kan haka. An sha kawo min irin waɗannan yaran kuma in bincika a gano ba almajirai ba ne. 

Kawo yanzu waɗanne matsaloli ne qungiyar ku ta gano kuma ta ke aikin kawar da su? 
To, akwai matsaloli da dama. Ka ga dai akwai ita wannan matsala ta shigar mabarata da ba almajirai ba, cikin harkar almajiranci, abin da ke jawo mana baƙaƙen maganganu da zagi. Sannan akwai matsalar yadda za a fahimtar da su kansu almajirai muhimmancin zama a makaranta,  kula da tsafta, da kula da lokutan karatu, yadda za a riƙa fifita karatun ba fita yawon neman abinci ba. Su ma kuma iyayen yara su fahimci cewa yanzu lokaci ya canja, ba irin yadda aka saba a da ba ne. Ko da yake na san iyaye da dama da ke ba da yaransu su je karatu don neman haddar Alƙur’ani ba wai sun rasa yadda za su kula da yaran ba ne, wallahi suna yi ne kawai don kwaɗayinsu na samun haddar, ba don sun kasa kula da yaran ko ɗaukar nauyin su ba. 

Wacce rawa ku ke buƙatar gwamnati ta taka wajen kawo gyare gyaren da ku ke buƙata? 
Eh, gaskiya ne. Muna da buƙatarsa hannun gwamnati sosai a wannan tsari da muka ɓullo da shi, domin mu ma ‘yan ƙasa ne, muna da haƙƙi a kula da mu, kamar yadda ake kula da wasu ɓangarorin. Ko da ba a fito an ba mu tallafi ba, a ba mu abin da ya kamata mu samu, a matsayin mu na ‘yan Nijeriya. Ko da ya ke mu ana yi mana kallon gidadawa marasa wayewa, ba mu san mai ake yi ba. Amma idan matsala ta taso mu ake tarawa a ce ana so a yi wa ƙasa addu’a. 

A lokacin tsohuwar gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan an vyullo da shirin inganta ilimin tsangaya, ina aka kwana ne a kan wannan tsarin?
Eh, gaskiya wannan babban abin takaici ne sosai. A ce wanda ba Musulmi ba, shi ne zai zo ya inganta maka abin da shi ya ke ganin bai shafe shi ba. Amma sai ga wata gwamnati ta zo da muke ganin ta Musulmi ce ɗan Arewa, ta yi watsi da tsarin, wannan abin kunya ne sosai. Ko babu komai Goodluck Jonathan ya mutunta mu ya nuna mu ma mutane ne masu daraja. Ko da a tsaya kan gine ginen makarantun tsangaya da aka inganta, ba za a manta da gudunmawar da Jonathan ya bayar ba. Ya kamata bayan tafiyarsa, waɗanda suka zo bayan sa sun ɗora daga abin da ya bari. Kuma dama wannan shi ne tsarin gwamnati. Amma ba su yi hakan ba. 

Wanne saqo Malam ke da shi ga mutane irin su tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso, da aka rawaito yana sukar harkar almajiranci da yadda ya danganta almajirai da ta’addanci? 
To, da farko dai ina son in shaida wa duniya cewa, ba ma jin daɗin yadda mutane ke fitowa kafafen watsa labarai da zaurukan sada zumunta suna faɗar maganganu a kan harkar almajiranci, da wanda ya isa ya yi magana da wanda bai isa ba. Kamar ita jarumar finafinan Hausa da aka ce ta yi wasu maganganu, wanda zan iya bata uzuri kan cewa, jahilci ne da rashin sani. Domin idan da ta san menene Alƙur’ani ba za ta yi maganganun da ta yi ba. Amma ga shi Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso wannan abin takaici ne sosai, ganin cewa, a matsayin sa na tsohon Gwamna kuma tsohon ministan tsaro ya fito yana danganta matsalar taɓarɓarewar tsaro kan almajiranci, abin baƙin ciki ne sosai. Idan ma wani bai sani ba, ya kamata shi Kwankwaso ya fi kowa sani, tun da mahaifinsa babban hadimin Alqur’ani ne, kuma ya daɗe yana yi wa almajirai hidima. Na kasance ɗaya daga cikin manyan masoya Kwankwaso, amma daga ranar da na ji abin da ya faɗa a kan almajirai, na ji duk ya fita a raina, fostocinsa da waƙoƙi da maganganunsa da na ke da su a wayata da gidana duk na ƙona su, na share na wayata. Saboda mu wannan ita ce rayuwarmu, mutuncin mu a nan ya ke, da mu da iyalan mu. Kuma lallai muna buƙatar ya fito ya nemi yafiyar mu, tare da janye kalamansa, domin babu wani almajiri da ya ji daɗin abin da ya yi. 

A ƙarshe wanne saƙo Malam ke da shi ga sauran alarammomi da iyayen yara almajirai? 
To, babban saƙon da zan isar ga sauran alarammomi shi ne haɗin kai, dole ne mu fito mu haɗa kan mu, mu kare mutuncin Alƙur’ani da karatun tsangaya, mu kuma ɗauki matakan da suka dace da zamani, domin inganta tsarin tafiyar da tsangayun mu da almajiran da aka ba mu amanar riƙewa. Su kuma iyaye ya kamata su fahimci cewa, yanzu zamani ya canja, dole ne su tsayu sosai wajen tallafawa makarantu kan al’amarin karatun ’ya’yan su. 

Mun gode.
Ni ne da godiya.