Mece ce kulawa a zaman aure? (1)

Daga AISHA ASAS

Na ci karo da wani rubutu da ya ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ya ɗauki hankalina izuwa wannan rubutu, ba don komai ba sai don zamewarsa bulaliya ga wata ɗabi’a da mata musamman na hausawa suka maida jiki. Kafin komai, bari mu ji wannan labari da za a iya kira kukan kurciya.

Wani ne ya ɗauki matarsa suka je gidan Zoo don kallon dabbobi. Karon farko suka ci karo da Biri da matarsa suna wasa irin ta masoya, cikin shaƙqi matar ta ce, kaga masoya.

Gaba kaɗan suka hango zaki da zakanya suna zaune, zakin ya kawar da kai yana sha’anin sa tamkar matar ba ta wurin. Matar wannan mutumin cike da tausayawa matar zakin ta ce, Allah sarki, rayuwa ba tare da kulawa akwai baƙin ciki.

A daidai wannan lokaci ne mijin na ta ya ce, ɗauki dutse ki jefa wa matar zakin nan sai ki yi kallo ko zai damu. Ba musu matar ta aikata, sai dai abin mamaki a wurinta isar dutsen ke da wuya, zakin ya miƙe yana gurnani alamun an tava abin da yake da matuƙar muhimanci gare shi kuma a shirye yake don yin faɗa da duk wanda zai taɓa lafiyarta.

Maigidan na ta bai gushe ba yana ƙara cewa gareta, ki maimaita abin da kika yi ga matar zaki ga matar biri. Tana jefa dutsen sai al’ajabi ya kamata, ganin birin mai nuna so da kulawa ga matarsa cikin hanzari ya gudu ya bar matar yana mai yi mata dariya.

Abin da ya sa na kawo  wannan ɗan labarin shine, ɗauke yake da darasin da ya kamata a ce mata sun hankalta sun yi wa kansu karatun tanatsu, sun fita daga duhun kai kan sahihiyar ma’ana ta kulawa.

Masana ilimin Nafs sun karkasa mutane zuwa gida uku a ɓangaren kulawa, inda suka tabbatar ba lallai sai mutum ya nuna kulawa irin ta wasan kwaikwayo ne sannan yake son matarsa ba. A wannan zamani da yawan mata kallon finafinai ko karatun littafai kan ruɗar dasu, sun kasa fahimtar ba ire-iren kalamai da aikatau da ake yi a fim ba ne kawai kulawar da ke nuna soyayya ba.

Kamar yadda aka hallici mutane da bambancin hali ko kama, haka aka halicci masu irin yanayin yadda suke bayyana soyayyarsu. Akwai mutanen da duk abin da suke so, to fa ba su da kwanciyar hankali har sai duniya ta san da irin son da suke masu. A kullum ƙoƙarinsu bayyana sirrin zuciyarsu ga abokin tarayyarsu a soyayya. Wannan hali ne, kuma ba wai hakan ba shi da kyau ba, asalima sau da yawa irin wannan kulawar kan riƙe aure ko da kuwa akwai ababen da ka iya kawo rabuwa a cikin sa. Sai dai waɗannan nau’in mutane ba su cika zama akan furucinsu ba, ba wai na ce dukka ba, akwai tsiraro da ke zama kaifi ɗaya, ba tare da gaba a samu wani sauyi ba.

Sai dai a iya fahimta ta, da yawa cikin waxannan mutane suna da buɗaɗɗiyar zuciya, wadda ke karɓar soyayya lokaci lokaci, ma’ana dai a kowanne lokacin tsuntsun na su zai iya tashi daga kan wata zuwa na wata. Wasu da dama daga cikinsu wawaye ne akan kulawa, ta inda a duk inda suka samu wata ta fara nuna masu irin kulawar da suke so, sai kiga sun fara bata hankalinsu ko da kuwa basa sonta irin ta gida.

Kuma a wannan ɓangaren ne ɓata garin maza ke yin basaja cikinsa don yaudarar mata. Da irin wannan kulawar ce za ka yaudari budurwa taba ka kanta, saboda ita ta amince ba wata hanya ta nuna so da wani zai mata da takai wadda kake nuna wa, don haka zuciyarta za ta amince kai ɗin ne masoyinta na gaske, kuma kana mata son da ba za ka iya rayuwa ba tare da ita ba, don haka me za ta yi inba taba ka tukuici da abin da ka nuna kana muradi, tunda dai ta san kun zama ɗaya, ba za ka gujeta ba. To a daidai lokacin da ya ɗirka mata ciki ya gudu ne za ta gano shayi ruwa ne, madara ake saka masa ya yi kauri.