Kamfanonin jiragen sama sun janye aniyar shiga yajin aiki

Daga BASHIR ISAH

Kamfanonin jiragen sama sun janye aniyarsu ta soma yajin aiki a ranar Litinin sakamakon tsadar mai da suke fuskanta.

Bayanin janye aniyar na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kamfanonin suka fitar a Legas ranar Lahadi.

Kamfanonin sun ce za su soma sabuwar tattauna tare da gwamnatin domin samar da maslaha mai ɗorewa.

Sanarwa ta ce, “Kamfanonin Jiragen Sama na Nijeriya (AON) na sanar da al’umma cewa, sakamakon kiran da manyan jami’an gwamnati suka yi musu da kuma alƙawarin share musu hawayensu da aka yi dangane da matsalar tsadar mai, sun janye aniyarsu ta shiga yajin aiki.

“Haka nan, mun tattauna a kan yadda za mu ci gaba da jagilar kwastomominmu yayin da muke ci gaba da tattauna da hukumomin da lamarin ya shafa.

“Duba da dukkan abubuwan da suka wakana da kuma yanayin tattalin arziki da tsaron ƙasa, AON na mai sanar da al’umma cewa ta janye sanarwar da ta fitar ran 9 ga Mayu na shirin dakatar da harkokinsu.”

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa, wasu mambobi shida na AON ne suka rattaba hannu a sanarwar janye aniyar tasu, da suka haɗa da Alhaji Shehu Wada Babban Daraktan Max Air; Dr Obiora Okonkwo, Shugaban Kamfanin United Nigeria Airlines; Capt. Roy Ilegbodu na Arik Air.

Sauran su ne, Capt. Abdullahi Mahmood na Aero Contractors; Alhaji Faisal Abdulmunaf na Azman Air da kuma Mr Allen Onyema Shugaban Air Peace.

Idan dai za a iya tunawa Blueprint Manhaja ta ruwaito yadda AON suka shirya shiga yajin aiki a wannan Litinin ɗin saboda matsalar tsadar mai da ta addabe su.