Tambuwal ya maka gwamnatin Sokoto kotu bisa ƙin bayyana rahoton kwamitin bincikensa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya shigar da ƙara kan Gwamnatin Jihar Sakkwato kan zargin ƙin miƙa masa rahoton Kwamitin Bincike na Shari’a da aka kafa domin binciken ayyukan gwamnatinsa.

Tambuwal, wanda a yanzu yake wakiltar Mazaɓar Sakkwato ta Kudu a Majalisar Dattawa, ya mulki jihar daga shekarar 2015 zuwa 2023. A cikin ƙarar mai lamba SS/133/2026, wadda aka shigar a gaban Mai Shari’a Mohammed Mohammed na Babbar Kotun Jihar Sakkwato, reshen mai lamba 6, tsohon gwamnan na neman kotu ta umarci gwamnatin jihar ta ba shi kwafin rahoton kwamitin.

Tambuwal ya shigar da ƙarar ne ta hannun lauyansa, U. O. Sule, SAN. Waɗanda aka ƙara sun haɗa da Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu; Babban Lauyan Jihar Sakkwato kuma Kwamishinan Shari’a; da kuma Kwamitin Bincike na Jihar Sakkwato.

Gwamnatin Aliyu ce ta kafa kwamitin, wanda tsohon Babban Alƙalin Jihar Gombe, Mai Shari’a Mu’azu Pindiga, ya jagoranta, domin gudanar da bincike kan ayyuka, mu’amalolin kuɗi da sauran al’amuran da suka shafi mulkin Tambuwal na tsawon shekaru takwas. Kwamitin ya gudanar da zaman sauraron bayanai da bincike, daga bisani ya miƙa rahotonsa ga Gwamnatin Jihar Sakkwato

Sai dai Tambuwal ya yi zargin cewa gwamnatin jihar ta ƙi ba shi kwafin rahoton, duk da cewa ya halarci zaman kwamitin tare da bayar da gudunmawarsa ga binciken. A cikin takardar fara shari’ar, tsohon gwamnan ya nemi kotu ta bayar da umarnin tilasta wa waɗanda ake ƙara su miƙa masa rahoton, domin ya san sakamakon binciken da kuma shawarwarin da kwamitin ya gabatar dangane da gwamnatinsa.

Tambuwal ya bada hujjar cewa, kasancewar ya miƙa kansa ga binciken tare da shiga cikin tsarin gudanar da shi, doka da kuma ƙa’idar adalci ta ɗabi’a sun ba shi damar sanin sakamakon binciken. Ya kuma ce riƙe rahoton na iya tauye masa damar kare kansa idan har kwamitin ya gabatar da wasu shawarwari ko bincike marasa kyau a kansa.

A cewarsa, samun rahoton ya zama wajibi domin ya shirya martaninsa tare da amfani da haƙƙinsa na tsarin mulki na samun damar sauraron ƙorafinsa cikin adalci, idan kwamitin ya gabatar da wasu shawarwari da suka shafe shi.

ƙarar ta mayar da batun rahoton kwamitin da aka daɗe ana jira gaban kotu, yayin da tsohon gwamnan ke neman taimakon shari’a domin tilasta fitar da rahoton. Kotun ta sanya ranar 9 ga Nuwamba, 2026 domin fara sauraron ƙarar.

By ukarofi

Leave a Reply