Gwamnatin Tarayya ta biya bashin albashin watanni takwas da SSANU ke bi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta saki kuɗaɗen albashin watanni takwas da mambobin ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’in Nijeriya (SSANU), domin daƙile barazanar shiga yajin aikin da ƙungiyar ke yi.

Kwanan nan SSANU ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki 14, inda ta buƙaci a gaggauta biyan sauran bashin albashin da ya taso sakamakon aiwatar da yarjejeniyar FGN/SSANU ta shekarar 2026.

ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa idan Gwamnatin Tarayya ba ta cika buƙatunta cikin wa’adin da ta bayar ba, za ta tilasta mata fara “cikakken yajin aiki mara iyaka” ba tare da ƙarin sanarwa ba.

Da yake magana da manema labarai a Abuja ranar Laraba, Shugaban SSANU, Mohammed Ibrahim, ya yaba wa Gwamnatin Tarayya bisa gaggawar amsa buƙatar ƙungiyar, yana mai cewa wannan mataki zai taimaka wajen ci gaba da zaman lafiya a harkokin aiki a jami’o’in ƙasar.

Ya kuma yaba wa Ministan Ilimi, Tunji Alausa, bisa shiga tsakani cikin gaggawa da kuma ƙoƙarin da ya yi wajen ganin an saki kuɗaɗen bashin albashin.

Ibrahim ya ce wannan ci gaba ya nuna cewa tattaunawa mai ma’ana tsakanin gwamnati da ƙungiyoyin ma’aikatan jami’o’i na iya haifar da kyakkyawan sakamako idan aka haɗa ta da ɗaukar mataki cikin gaggawa.

“Wannan shaida ce cewa tattaunawa mai ma’ana, idan aka haɗa ta da ɗaukar mataki cikin gaggawa, na iya kare zaman lafiya a harkokin aiki da kuma jin daɗin ma’aikata,” inji Ibrahim.

Ya buƙaci mambobin SSANU a faɗin ƙasar da su tuntubi hukumomin jami’o’insu domin tabbatar da cewa an biya kuɗaɗen da aka saki cikin gaggawa kuma yadda ya kamata.

Shugaban SSANU ya kuma umurci mambobin ƙungiyar da su kai rahoton duk wani gibi ko rashin daidaito da suka lura da shi wajen biyan kuɗaɗen ga ƙungiyar domin ɗaukar matakin da ya dace.

Ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta ci gaba da wannan salon mayar da martani cikin gaggawa wajen aiwatar da yarjejeniyoyin da aka cimma da ƙungiyoyin ma’aikatan jami’o’i, tare da biyan sauran haƙƙoƙin da ake bin ma’aikata.

Sai dai Ibrahim ya jaddada cewa har yanzu gwamnati na da sauran albashin watanni biyu da aka riƙe a lokacin yajin aikin shekarar 2022, da kuma bashin shekara guda da ya taso sakamakon ƙarin albashin kashi 25 da kashi 35 cikin 100.

“Waɗannan haƙƙoƙin halastattu ne na mambobinmu, kuma bai kamata a sake jinkirta biyan su ba,” inji shi.

Ibrahim ya kuma buƙaci gwamnatocin jihohi da kwamitocin gudanarwa na jami’o’in jihohi da su tabbatar da cikakken aiwatarwa tare da samar da isassun kuɗaɗen aiwatar da yarjejeniyoyin da aka cimma da ƙungiyoyin ma’aikatan jami’o’i.

Ya ce aiwatar da yarjejeniyoyin ta hanyar fifita wasu ko jinkirta su na iya haifar da sabon tashin hankali tare da kawo cikas ga zaman lafiya a harkokin aiki a tsarin jami’o’in ƙasar.

Ibrahim ya sake tabbatar da cewa ƙungiyar za ta ci gaba da bin hanyar tattaunawa mai ma’ana da kuma tabbatar da zaman lafiya a harkokin aiki, amma ya ce za ta yi amfani da hanyoyin da doka ta tanada wajen kare haƙƙoƙi da jin daɗin mambobinta.

Ya ce sakin bashin albashin ya ƙara ƙarfafa gwiwar ma’aikata cewa tattaunawa mai ma’ana na iya haifar da sakamako a aikace ga ma’aikata, ɗalibai da kuma tsarin jami’o’in Nijeriya baki ɗaya.

By ukarofi

Leave a Reply