Tsoffin sojojin yaƙin basasa ba su cancanci biyan fansho ba, Inji Hukumar Fansho ta Soja

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar fansho ta soji, ta ce, tsoffin sojojin da suka yi yaƙi a ɓangaren gwamnatin Nijeriya a lokacin yaƙin basasa ba su da haƙƙin karɓar fansho duk wata.

Tsoffin sojojin sun zargi gwamnatin tarayya da rashin biyansu haƙƙoƙinsu tun bayan barin aikin soja kimanin shekaru 44 da suka gabata.

Kakakin hukumar, Laftanar Olayinka Lawal, ya ce, sojojin da suka yi ritaya ba su kai shekaru 15 da dokar fansho ta kayyaɗe ba da kuma ƙa’idojin da suka dace da rundunar sojin Nijeriya don samun cancantar abin da suke buƙata.

Ya ƙara da cewa, ɗaya daga cikin jagororin ƙungiyar Sajan Kasali Busari, an ƙara masa ƙarin shekarun hidima saboda shiga yaƙin, amma har yanzu ya kasa cika shekarun da aka kayyaɗe domin samun cancantar biyan fansho duk wata.

Tsoffin sojojin, a ƙarƙashin inuwar ƙungiyar farko da ta yi ritaya ko kuma ta sallame su na tsawon shekaru goma ko sama da haka a aikin soja, sun kuma ce hukumar fansho ta soja ta ke cire su daga biyan fansho, kuma ƙoƙarin shigar da su bai yi nasara ba.

Kodinetan ƙungiyar na ƙasa, Babawande Philips, ya sha alwashin fara zanga-zanga a faɗin ƙasar a ranar Laraba domin amsa buƙatunsu.