Gwamnatin Tarayya ta roƙi kamfanonin jiragen sama bisa shirin dakatar da zirga-zirga

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ministan Sufurin Jiragen Sama na Nijeriya, Sanata Hadi Sirika, ya roƙi kamfanonin jiragen sama na Nijeriya da su dakatar da shirinsu na dakatar da ayyukansu daga yau Litinin saboda tsadar man fetur daga Naira 190 zuwa Naira 700 kan kowace lita.

Sirika ya yi wannan roƙo ne a wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin jama’a, Mista James Odaudu ya fitar ranar Asabar a Legas.

Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya ya bayar da rahoton cewa, kamfanonin jiragen sama na Nijeriya a ƙarƙashin inuwar kamfanin Airline Operators of Nigeria (AON), a ranar Juma’a sun sanar da shirin dakatar da ayyukansu daga ranar Litinin saboda tsadar man jiragen ke yi.

Ministan ya buƙaci kamfanonin jiragen da su yi la’akari da yawan tasirin rufe ayyukan da zai yi ga ‘yan Nijeriya da matafiya a duniya.

Ya ce: “An jawo hankalin Ministan Sufurin Jiragen Sama, Sanata Hadi Sirika kan rahotannin da ke cewa tsarin sufurin jiragen sama na ƙasar zai lalace tun daga ranar Litinin.

“Wannan ya biyo bayan barazanar da kamfanonin jiragen sama suka yi na rufe sufurin sama a cikin gida Nijeriya,” in ji sanarwar.