An samu sabbin nutane 169 da suka kamu da COVID-19 a babban yankin Sin

Spread the love

Daga CMG HAUSA

Bisa alƙaluman da hukumar kula da lafiyar ƙasar Sin ta fitar sun nuna cewa, an samu mutane 169 da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a babban yankin ƙasar a ranar Asabar.

Daga cikin adadin, 157 na da alaƙa da yada cutar a cikin gida, sannan 12 kuma daga ƙetare.

An samu jimillar sabbin kamuwa da cutar 729 waɗanda ba su nuna alamomin kamuwa da cutar ba a ranar Asabar, yayin da adadin majinyatan da ba su nuna alamun kamuwa da cutar ba 37,636 suke ƙarƙashin kulawar jami’an kiwon lafiya.

Kawo yanzu, adadin mutanen da aka tabbatar sun taba kamuwa da cutar COVID-19 a babban yankin ƙasar Sin ya kai 223,145, sannan jimillar mutane 5,222 annobar COVID-19 ta kashe a ƙasar.

Fassarawa: Ahmad

By Editor