Sharhi: Kafofi na wai masu ‘yanci

Spread the love

Daga LUBABATU LEI

Kwanan nan, Ministan Watsa Labarai da Raya Al’adu na Najeriya Lai Mohammed, ya ja kunnen kamfanoni mamallaka dandalolin sada zumunta, da su daina bai wa ƙungiyar nan ta IPOB, ta ‘yan aware dake kudancin Najeriya, damar yaɗa bayanai na rura wutar rikici da ƙabilanci a kan shafukansu.

Lai Mohammed ya yi wannan gargaɗi ne a yayin wata tattaunawa da tawagar kamfanin Facebook. Ya ƙara da cewa, Gwamnatin Najeriya za ta sanya ido sosai kan shafukan Facebook da sauran dandaloli makamantan sa a kwanaki masu zuwa, domin tabbatar da ko facebook ɗin ya kiyaye wannan jan hankali, yayin da ƙasar ke ƙara azamar yayata manufar amfani da dandalolin sada zumunta ta hanyoyin da suka kamata.

A cewar sa, an riga an ayyana ƙungiyar IPOB a matsayin ta ‘yan ta’adda, don haka babu wani dalili da zai sa Facebook ya riƙa bai wa ƙungiyar damar shiryawa, ko gabatar da farfagandar ƙiyayya, ko wargaza zaman lafiyar Najeriya.

Idan ba a manta ba, a bara, gwamnatin Nijeriya ta dakatar da ayyukan shafin sada zumunta na Twitter a faɗin ƙasar, sakamakon yadda kafar Twitter ya goge wani saƙon da Shugaban Nijeriya Mohammadu Buhari ya wallafa ta kafar, inda ya gargaɗi masu tada rikici a ƙasar. Bayan da Twitter ya goge saƙon Shugaba Buhari, Ministan Yaɗa Labarai da Raya Al’adu na ƙasar, Lai Mohammed ya zargi Twitter da nuna fuska biyu, bisa ga yadda ya goge saƙon shugaban, amma ba tare da ɗaukar wani mataki kan saƙonnin da jagororin ‘yan aware a Nijeriya suke wallafawa ba. Ya ƙara da cewa, a lokacin da mutane suke kona ofisoshin ‘yan sanda tare da kashe su yayin zanga-zangar End SARS, a ganin Twitter, suna da ‘yancin gudanar da zanga-zanga. Amma a lokacin da makamancin lamarin ya faru a Amurka, sai ya zama tawaye.

Sai dai hakan ba kawai ke faruwa a Nijeriya ba. Yayin da aka samu matsalar gyara doka a yankin Hong Kong a shekarar 2019, shahararrun kafofin sada zumunta na ƙasar Amurka kamar su Twitter da Facebook da sauransu sun taba dakatar da shafukan masu amfani da kafar sama da dubu ɗaya bisa dalilin wai suna ba da labaran karya ko suna samun goyon bayan gwamnatin ƙasar Sin, amma haƙiƙa kafofin sun gabatar da labarai na haƙiƙa da suka faru a yankin Hong Kong. A sa’i ɗaya kuma, kafar Twitter ba ta kula da sakwannin da suke shafa wa ‘yan sandan Hong Kong da gwamnatin ƙasar Sin bakin fenti ba.

Irin wannan abubuwa ba sa lisaftuwa. Matsayin da kafofi irnsu Facebook da Twitter suka ɗauka ya dogara ne ga rukunonin da ke mara mata baya, kuma moriyar ƙasar Amurka ce kafofin ke wa aiki, a maimakon a ce su kamfani masu zaman kansa. A ƙasashen Afghanistan da Iraki da Syria da Libya da sauransu, Amurka ta yi ta tada zaune tsaye da mara wa masu adawa da gwamnati baya, don cin moriyarta, kuma kafofinta na yanar gizo ma suna ba da taimako.

Mai Zane:Mustapha Bulama

By Editor