Da gaske ba zaratan sojoji a Nijeriya?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Bayan samun ’yancin Nijeriya a 1960, an samu gwamnatin farar hula ne, wato Jamhuriya ta Farko, da marigayi, Sir Abubakar Tafawa Ɓalewa ya jagorantar a matsayin Firaminista yayin da Marigayi Nnamdi Azikwe ke matsayin Shugaban Ƙasa, da hakan ya faru gabanin ɗaukar tsarin shugaba ɗaya mai wuƙa da nama irin na Amurka da a ka yi amfani da shi a jamhuriya ta biyu daga 1979.

A wancan lokacin an yi amanna aikin soja shi ne yaƙi don kare ƙasa ba wai riƙe madafun mulki na gwamnati ba. Hasalima ai sojojin Nijeriya na cikin sojojin da su ka tafi yaƙin duniya a ka gwabza da su kuma su ka yi abin kirki.

Duk tarbiyyar da a ka yi mu sui ta ce ta kare ƙasa daga ko taron ƙasashen da ke da manufa ɗaya don kafa duniya bisa hulɗa da juna a tsarin diflomsiyya, tattalin arziki, ilimi da mutunta addini da al’adu. A gwagwarmyar neman ’yanci, zaratan farar hula ne da ba tare da riqe bindiga ba su ka yi ta yaɗa muradun samun ’yanci wanda kuma ƙarshe a ka samu nasara a ka kuma damƙa ’yancin a hannun su. Farar hula da soja na buƙatar aiki tare don tabbatar kasancewar ƙasa a dunƙule.

Idan gwamnatin farar hula na fargabar kutsen sojoji to zai yi wuya su maida hankali wajen gudanar da aiki yadda ya dace. Ba mamaki ka ga a na ta ba wa manyan jami’an soja fifiko don gudun samun saɓani.

A gefe guda za ka ga mutane na da azalzala cewa gwamnati ta canja manyan hafsoshin don tunanin ba mamaki hakan ke kawo kwan-gaba-kwan-gaba a tabbatar da tsaro. Ba lalle ne mutane su fahimci dalilan gwamnati na yin bakam kan irin waɗannan lamura don tsaro abu ne na sirri da kowa wane bayani ne a kan bayyana ba duk kuwa matsin lambar da mutane su ka yi ko za su yi.

Idan a ka duba tarihin Nijeriya daga 1960 zuwa yau kusan an yi canjaras tsakanin yawan mulkin gwamnatocin soja da na farar hula. Wani abin dubawa a cikin mulkin farar hular ma tsoffin sojoji da su ka yi mulkin soja su ka sake dawowa su ka sa farar hula su ka yi mulki na kimanin rabin shekarun da farar hula na asali su ka yi kan mulki. Zuwa yanzu dai za a iya cewa mulkin dimokraɗiyya ya yi dogon zango a kan mulki tun 1999 ba katsalandan.

Abun fahimta dai muhawara ba za ta kare ba kan abubuwan cigaba da gwamnatin farar hula ko ta soja ke kawowa ƙasa. Bambancin soja na jingine tsarin mulki yayin da farar hula ke amfani da tsarin mulkin ko da kuwa ba a bin dokokin sau da kafa.

Wasu matakan da sojoji kan ɗauka na gaba gaɗi kamar ƙirƙiro jihohi da ƙananan hukumomi ba ya samuwa a farar hula. Kazalika sojoji kan iya tura kantomomin soja jihohi daban da jihohin su na asali da hakan kan taimaka wajen rage hamayyar ƙabilanci ko wariyar yanki da sauran su.

Fararen hula na amfani da gwarzantaka wajen nuna kishin ƙasa da kare ƙasa daga duk wata barazana. Yayin da soja ke amfani da makamai don yaƙin kare ƙasa fararen hula kan yi amfani da alƙalami da harshe wajen kare muradun ƙasa.

Haƙiƙa idan lamura su ka rikice nan take a ke ɗaukar farar hula a yi ma sa horarwar gaggawa don riqe makamai su tafi bakin daga. Yaƙin basasar Nijeriya na daga misalan wannan yanayi da farar hula su ka zama dakarun dare ɗaya. Ko ma dai me za a ce bambancin farar hula da soja shi ne horarwar dabarun yaƙi da a kan koyawa sashen farar hula masu ƙoshin lafiya da hakan kan ba su damar riƙe makami da sarrafa shi bisa umurnin yin hakan ko kuma in an tafi bakin dagar yaƙi. 

Ba a yi tunanin wasu sojoji a Nijeriya za su kifar da gwamnatin ’yan gwagwarmayar kwatawa Nijeriya ’yanci ba. Ba ma haka kaɗai ba, sojojin sun yi mummunan kisan gilla ga manyan jigogin ’yancin Nijeriya. Wannan mummunan akasi ya afku ne a 1966 tsakanin Legas da Kaduna.

Zubar da jinin waɗannan dattawan kuma farar hula ya jawo rabuwar kawuna a tsakanin ’yan Nijeriya da ma sojojin kansu. Tun a lokacin a ka ƙarfafa bambancin ƙabila da yanki. Waɗannan sojojin sun sauka daga aikin da a ka ɗauke su, sun juya bakin bindigarsu sun harbe shugabannin ƙasar da ya dace su kare.

Mai kare ƙasa da jagororin ƙasa ya juya bakin wutarsa ya banka wa jagororin ƙasar kuma har ya na ganin abin da ya aikata daidai ne! kun ga hakan shi ya kai ga ƙasar ta afka yaƙin basasa daga bisani wajen ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane da lalata dukiya da jefa mata da yawa shiga karuwanci don samun abinci.

Gaskiya in mu ka bi diddigin wannan fitina ta zubar da jini, ta maida Nijeriya tamkar ba ƙasa ɗaya ba. A yanzu ba akwai inda babbar kasada ce wani ɗan ƙasa daga wani vangare ya shiga wani ɓangaren ƙasar. Laifin da kansa a harbe mutum ko sare kan sa, shi ne shi ba asalin ɗan wannan yankin ba ne ko kuma dan yankin ne amma da alamu ya na hulɗa da ɗan wani yanki.

A kwana a tashi sai bambancin addini ma ya zo ya shiga inda za ka ga an tare mutum don ba addininsa ɗaya da waɗanda su ka tare shi ba, sai su kashe shi kuma su na zaton za su zauna lafiya ba abin da zai biyo baya. Sojojin nan sun aikata babban laifi kuma a matsayin darajar aikin su na kare ƙasa da talakawan ƙasa, da zarar sun aikata wani abu akasin aikin da ya dace su yi sau ka ga an samu saɓanin da sai gyaran Allah. Wani ginshiƙin da kan kawo nasara da cigaban ƙasa shi ne ƙare doka da oda.

Tabbatar da bin doka ko da kuwa ta danjar alama ce ta kan titi, na kawo cigaban tattalin arzikin ƙasa. Keta ƙaramar doka na iya kawo hatsarin da zai iya shafar wanda bai ji ba kuma bai gani ba.

Baya ga juyin mulkin da sojoji su ka zubar da jini a 1966, an ƙara samun wani dalilin da ya kawo koma baya ga sojojin Nijeriya. Ba ma sojoji kaɗai ba har wasu jami’an tsaro hakan ya shafe su. An sha zargin jami’an tsaro da aikata wasu ayyuka da su ka zama cin zarafin waɗanda ba su aikata laifin komai ba. Idan an samu masu laifi a ka kaucewa hukunta su don wataƙila su na da uwa a murhu ko su na da hanyar fitar da kan su daga sarƙa, sai kuma a ka samu wasu da maimakon a gargaɗe ko a yi mu su sulhu a kan wani saɓani, sai ya kai ga buɗe wuta, hakan na kawo babbar matsalar rashin girmama juna tsakanin ’yan ƙasa da jami’an tsaro.

Tsohon babban mai kare lafiyar marigayi shugaban mulkin soja na Nijeriya Janar Abacha, wato Manjo Hamza Almustapha, ya ce, Nijeriya ba ta da zaratan sojoji, don yadda a ka yi sakaci kan hakan tsawon shekaru.

Sakacin da ya ce ya kawo koma baya da maida jami’an tsaro su ka zama na tsoro! A wani wajen ma jami’an kan zama masu ɗaukar matakin ihun bayan hari. Wani lokacin a kan budurwar soja da ta yi wa wani farar hula rasar kunya har ya mare ta, sai ka ga soja ya gayyato abokan aikin sa sun shigo su na ta dukan fararen hula da yi mu su barazanar halaka su har ma da kama wasu su yi mu su rotse.

A na tsammanin a iya wannan yanayi bincike ya dace a gudanar ta hanyar miƙa batu ga ’yan sanda da a ka horar da su hulɗa da jami’an tsaro. Duk wanda yara sojoji su ka yi ma sa dukan kawo wuqa zai yi wuya har abada ya yafe hakan kuma don an ce sojoji na da amfani ba zai amince ba.

Manjo Almustapha wanda ya ke magana a wata zantawa ta musamman a Abuja, ya ce, barin sojoji da ’yan sanda a baya su ka yi aikin haɗin gwiwa na fiye da shekara ɗaya ya sa sojojin sun kwalance da ɗaukar ɗabi’u irin na ’yan sanda.

Almustapha ya ƙara da cewa, su kuma ’yan sanda sun sauya daga ayyukan kare fararen hula sun ɗauki wasu ɗabi’u na soja da hakan ya saka su ka sauka daga tsarin aikin su na hulɗa da farar hula. Don haka Almustapha ya buƙaci yin garambawul a lamarin sojoji da ’yan sanda don samun tsaro yadda ya dace. Shaharerren sojan ya nuna fargabar mallakar ma’adinai musamman zinari ya sa wasu ƙasashe ke yi wa yankin arewacin Nijeriya maƙarƙashiya.

Kammalawa:
Ya na da kyau a cusawa duk wani mai wata sana’a ko aiki na farar hula ko jami’in tsaro aƙidar ƙishin ƙasa da aiki bisa ƙa’idojin aiki. Hakanan, ya na da kyau a riƙa amfani da dokoki wajen ladabtar da waɗanda su ka zarme da gangan saboda gadararsu shafaffu ne da mai ba za a iya taɓa su ba.