An yi jana’izar mahaifin Sanata Sani Musa a Minna

Daga BASHIR ISAH

Jama’a daga sassan Nijeriya suka haɗu a Minna, babban birnin jihar Neja domin jana’izar mahaifin Sanata Mohammed Sani Musa.

An gudanar da sallar jana’izar marigayi Alhaji Musa Tanko (Iyan Minna) ne a fadar Sarkin Minna, Dr Umar Farouq Bahago a Larabar da ta gabata.

Daga cikin waɗanda suka halarci jana’izar har da Tsohon Shugaban Ƙasa na mulkin soja, Janar Abdulsallami A. Abubakar, wanda ya bayyana marigayin a matsayin tsayayyen mutum wanda rasuwarsa babban rashi ne ga al’umma.

A nasa ɓangaren Gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello, wanda ya jagoranci manyan baƙin da suka halarci jana’izar, ya ce marigayi Iyan Minna ya kasance uba, kaka kuma abin koyi ga jama’a da daman gaske, tare da cewa an yi rashin kyawawan shawarwarin da ya kasance yana bai wa jama’a a halin rayuwarsa.

Ya ce, “Wannan rashi ne babba, a halin rayuwarsa ya kasance tamkar uba ga mutane da yawa, kuma mutum ne mai dattaku. Za mu yi matuƙar rashin nagartattun shawawsrinsa. Ina roƙon Allah ya kyautata makwancinsa. Kana Ya bai wa ahalinsa dangana da haƙurin wannan rashi.”

Sanata Sani Musa shi ne sanata mai wakiltar shiyyar Neja ta Gabas a Majalisar Dattawan Nijeriya.