NLC ta dakatar da yajin aikin da ta soma a Kaduna

Ƙungiyar Kwadago ta Ƙasa (NLC) reshen jihar Kaduna, ta dakatar da yajin aikin gargaɗi na kwana biyar da ta soma a Litinin da ta gabata.

NLC ta ɗauki matakin dakatar da yajin aikin ne domin amsa gayyatar da Gwamnatin Tarayya ta yi mata ya zuwa Alhamis.

Shugaban NLC na ƙasa, Comrade Ayuba Wabba ne ya bayyana hakan ga manema labarai bayan wani taron gaggawa da suka yi a Kaduna a Laraba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *