Zanga-zangar Kaduna: Matan da El-Rufai ya ɗauko haya sun yi ƙorafin rashin biyan su haƙƙinsu, cewar NLC

A ranar Laraba Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) reshen jihar Kaduna, ta shiga yini na uku a ci gaba da zanga-zanga da kuma yajin aikin kwanaki biyar da ta soma a jihar don nuna rashin yardarta kan matakin korar wasu ma’aikatan jihar da Gwamna Nasir El-Rufai ya ɗauka.

Kamar yadda ta wallafa a shafinta na twita, NLC ta ce ta gano cewa Gwamna El-Rufai ya yi hayar wasu mata na musamman domin su shigo su lalata wa NLC tsarinta wanda a ƙarshe haƙarsa ta kasa cim ma ruwa. Sannan kuma matan, sun yi ƙorafin an bar su a yashe ba tare da biyan su ladan aikin da aka kwaso su su aikata ba.

Kalli wannan bidiyon na ƙasa: