Ana cece-kuce kan shugabancin ƙungiya tsakanin Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa da ’yan kasuwar Dawanau

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

’Yan kasuwar kayan abinci da ke Dawanau a Jihar Kano sun koka da yadda sama da shekaru ake ta jan ƙafa wajen gudanar da zaɓen shugabannin ƙungiyar ’yan Kasuwar wanda yanzu haka a sakamakon hakan ake tafiyar da ƙungiyar ƙarƙashin kwamitin riƙo da shugaban ƙaramar hukumar Dawakin Tofa ya kafa da kuma wani Shugabancin da suka gudanar da zaɓen ƙungiyar da Alhaji Mustapha Mai Kalwa yake jagoranta.

Binciken da muka yi ya nuna cewa, tsohon zaɓaɓɓen shugaban ƙungiyar ’yan Kasuwar da ya jagoranci ƙungiyar har karo Biyu, Alhaji Mustapha Mai Kalwa daga baya ya sauka aka yi kantononi riƙo daban-daban bisa sahalewa ƙaramar hukumar Dawakin Tofa ƙarƙashin jagorancin Alhaji Ado Tambai Ƙwa ta kafa da yanzu Alhaji Sani Ƙwa yake a matsayin kwamitin riƙo ya ɗauki lokaci bai iya gudanar da shirya zaɓen da tunda fari aka ce zai gudanar a cikin watanni uku ba, wanda aka riƙa ƙara masa wa’adin da yanzu ya shafe sama da shekara ɗaya.

Hakan ya sa damuwa sosai daga yawancin ’yan Kasuwar suke zargin tamkar akwai wani ƙulli na biyan buƙatar siyasa da ya sa ƙaramar hukumar Dawakin Tofa ƙarƙashin shugabancin Honarabul Ado Tambai Ƙwa ke jan ƙafa wajen tsayawa a gudanar da zaɓen a matsayinsa na mai wuƙa da nama a harkar tabbatar da yin zaɓen.

Kasuwar Dawanau kasuwa ce da ta yi suna a Duniya kan saye da sayarwar kayan abinci, domin ana zuwa daga Ƙasashen Afirka da Asiya har da Turai don yin mu’amalar kayan abinci.

Amma ana ganin kasuwar ta shiga wani yanayi na rashin tabbataccen shugaba domin kuwa bada jimawa ba, tsohon shugaban kasuwar Alhaji Mustapha Mai kalwa ya jagoranci yin wani zaɓen bisa samun izinin kotu aka sake bayyana shi a matsayin shugaban ƙungiyar kasuwar.

Wasu yan Kasuwar da dama da muka gana da su sun fi nuna gamsuwa akan a yi musu zaɓe a kasuwar don a sami haɗin kai, akwai mutane ’yan Kasuwar da suka cancanta za su iya jan ragamar Kasuwar da za su bada gudummuwa wajen cigabanta.

Wata majiya ta ce, rashin tsayawa a gudanar da zaɓen Shugabannin kasuwar ya ɗoru ne akan shugaban ƙaramar hukumar Dawakin Tofa Honarabul Ado Tambai Kwa wanda suke zargin ya yana naɗa kantoma na riƙo a kasuwar ne a matsayin dama ta muƙamin siyasa da zai tafi da shi, ba tare da an gudanar da zaɓe ba, har zuwa lokacin daf da ƙarshen wa’adin mulkinsa da yake a karo na biyu, sannan ne ake hasashen zai sa ayi zaɓen.

Kan wannan zarge-zarge da ake yi wa Shugaban ƙaramar hukumar Dawakin Tofa Honarabul Ado Tambai Kwa na cewa shine ke hana ruwa gudu ga gudanar da zaɓen yan ƙungiyar ’yan Kasuwar  Kasuwar  ta Dawanau ta yi musu katsalandan a cikin huruminsu. Mun tuntuɓe shi ya kuma musanta cewa akwai wata buƙata ta siyasa a rashin gudanar da zaɓen, illa kawai rashin cika ƙa’doji na yanayi da zai ba da dama a yi zaɓen daga tsohon zaɓaɓɓen shugaban kasuwar Alhaji Mustapha Mai Kalwa wanda har yanzu bai miƙa duk wasu muhimman takardun na ƙungiyar ga kwamitin riƙon kasuwar da suka samar ba, wanda hakan shi zai bada damar a yi zaɓen.

Ya ce, wata uku suka bai wa kwamitin riƙon da suka kafa da farko ya shirya yin zaɓen amma Mustapha Mai Kalwa bai ba su haɗin kai da ya kamata ba, ta miƙa musu muhimman takardun rijistar  ƙungiyar Kasuwar ba da hakan zai bada damar za a yi zaɓen.

Tambai ya tabbatar da cewa, ko gobe Alhaji Mai Mustapha mai Kalwa ya yarda shi ba Shugaba bane da yake iƙirari, ya miqa rijistar ƙungiyar za a gudanar da zaɓe koma wanene ’yan Kasuwar suka zaɓa ko Bayarabe ko Inyamuri ko Bature ne duk wanda suke so ya zo ya zama shugaban ƙungiyar Kasuwar ƙaramar hukumar za ta amince.

Ya yi zargin cewa, su Mustapha Mai Kalwa don biyan buƙatar su tuƙuru fassara  bunƙasar da karɓuwar kasuwar Dawanau ta kai wasu mutane Jihohin Neja da Nasarawa don sana’ar kayan abinci  har ma an kai wasu kasuwar Gezawa don a janye tasirin kasuwar, Dawanau amma ba su iya samun nasarar ƙasar da kasuwar Dawanau ba.

Shugaban ƙaramar hukumar na Dawakin Tofa Ado Tambai Ƙwa ya ce, Gwamnati da masarauta da ɓangarori na jami’an tsaro sun san da wannan magana na Shugabancin kasuwa kuma kasuwar Dawanau a cikin hurumin  ƙaramar hukumar sa take. Don haka a shirye suke su ba da dama a yi zaɓe in an cika ƙa’doji na ƙaramar hukumar.

Shima a ɓangarensa da muka tuntuɓe shi, Alhaji Mustapha Mai Kalwa ya ce, maganar ya yi ƙoƙarin lalata kasuwa da Shugaban ƙaramar hukuma ya yi ba ta da tushe, bare makama ta tsabagen son rai ce kawai, kuma shi ba bu wani abu da yake nema a wajen Shugabancin ƙaramar hukumar bare a shugabancin Kasuwar. Allah ne shaida a cikin harkar ƙungiya baya neman komai illa haƙƙin ’yan kasuwa da suke karewa da makomar su.

Ya ce, yanzu haka ma suna kotu kan wannan sai dai an zo wata gaba da ƙaramar hukuma ta ke neman masalaha da su domin an zauna da kwamishinan Kasuwanci na Jihar Kano don samun maslaha.

Ya yi nuni da cewa, su sun ma riga sun gudanar da zaɓen su a ƙungiyance bisa umurnin kotu, dama su ’yan kasuwa ne ƙungiya kuma ba ta ƙaramar hukuma bace. Amma ƙaramar hukuma ita ta ke da Kasuwar za ta karɓi haraji amma hurumin gudanar da shugabancin ƙungiyar ta ’yan kasuwa ce don haka ma suka yi wa ƙungiyar rijista ta ƙasa wacce kowa daga sashin ƙasar nan zai iya zama shugabanta muddin dai ɗan kasuwar ne.

Mai Kalwa ya ce, shekara da shekaru kowane Shugaban ƙaramar hukuma ya zo sai ya ce ya rushe shugabancin ƙungiyar kasuwa ya kawo na riƙo. Don haka suka ga bai kamata su barwa yan baya matsala ba don haka suka yi wa ƙungiyar rijistar CAC.

Alhaji Mustapha Mai Kalwa ya jaddada cewa, ba shida wani abu da yake nema akan shugabancin ƙungiyar kasuwar domin Allah ya rufa masa asiri suna wannan ƙoƙari na tabbatar da haƙƙin ’yan Kasuwar ne ta nema musu ’yancinsu da mutuncin su.