Da ɗumi-ɗumi: ASUU ta yi barazanar zuwa sabon yajin aiki, ta ba wa gwamnati wa’adin sati uku

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyar malaman jami’o’i ta Nijeriya (ASUU) ta bai wa gwamnatin tarayya wa’adin makonni 3 don cika ma ta sharuɗɗan da ta gindaya wa gwamnatin.

Ta bayyana wannan ƙudirin nata ne inda ta ce wajibi ne gwamnatin ta cika ma ta alƙawarran da suka sa hannu akai tun ranar 23 ga watan Disamban 2020.

ASUU ta ce, in har gwamnatin bata cika sharuɗɗan na ta ba cikin makonni 3 masu zuwa, za ta ɗauki tsattsauran mataki.

Har ila yau, ƙungiyar ta kafa kwamiti mai zaman kansa don bincike akan matsayin da aka bai wa ministan sadarwa.

Dama jami’ar tarayya ta kimiyya da ke Owerri ta ƙara wa ministan matsayi zuwa farfesa a ɓangaren tsaron yanar gizo.

Rashin gamsuwa da matsayin yasa ƙungiyar ASUU ɗin ta kafa kwamiti don bincike akan cancantar ministan.

Ku saurari ƙarin bayani …