Babbar jikar Sardauna, Hajiya Hadiza Shehu Kangiwa ta rasu

Daga IBRAHEEM HAMZA MNUHAMMAD

Allah Ya yi wa Hajiya Hadiza Shehu Kangiwa, babbar jikar jikar Sardauna, Ahmadu Bello rasuwa.

Aminiyar marigayiyar, Hajiya Binta Tafawa Balewa ta shaida wa Manhaja cewa, “Hajiya Hadiza Shehu Kangiwa, wacce mata ce ga marigayi tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato ta da, Alhaji Shehu Kangiwa.

“Ta kasance babbar jikar marigayi Sardauna Ahmadu Bello, kuma ‘yar fari ga Hajiya Inno Ahmadu Bello.

“Marigayiyar ita ce ‘yar marigayi Wamban Kano, Abubakar Ɗan Maje, kuma babban ɗa ga marigayi Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na 1.

“An haife ta ne a shekarar 1960, ta rasu ran Talata a Sakkwato, ta bar yara uku: namiji ɗaya da mata biyu.

“An yi marigayiyar Jana’iza bisa koyarwar addinin Islama a gidan Sardauna da ke kan titin Diori Hammani da ke Sakkwato.”

Ɗan’uwan marigayiyar, Alhaji Shehu Aliyu Maradun ya ce an yi babban rashi, domin Hajiya Hadiza ta na da son jama’a da sauƙin kai duk da darajar asalinta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *