Masarautar Wukari da Jukunawa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Kamar dai yadda kowa ya fi saninta da suna Wukari, ta kasance hedikwatar masarautar Wukari. Asalin sunanta shi ne Ukari, wacce kuma kalma ce ta Jukunanci, wacce ke da ma’ana ta ‘ka fifita’. Masarauta ce da aka kafa ta a shekarar 1596 bayan rushewar Daular Kwararrafa.

Tushe:
Bayan rushewar Daular Kwararrafa wacce ke da hedikwata a Api, sai Jukunawa waɗanda su ke tun asali su ne ke shugabanta waccar daula ta Kwararrafa suka matsa gaba zuwa wannan bigire, suka kafa garin da a yanzu ake kira Wukari. Ita kuwa wannan kalma ta Wukari, asalinta shi ne Ukari, wacce kuma kalma ce ta Jukunanci mai ma’ana ta ‘ka fifita’. Sarkin Jukunawa na 40, Aku Uka Katakpa, shi ne ya jagoranci wannan ƙaura a cikin shekarar 1596 (Adamu, 2016; Oleyede, 1996). Dukkan wanda ke shugabantar wannan masarauta, shi ake kira Aku Uka, kalmomin da ke da ma’ana ta sarkin da ya fifici kowane sarki a duniya; wato sarkin da ya fi kowane sarki a duniya (Adamu, 2016).

Wannan gari shi ne ya zamo tubulin canjin tarihin Jukunawa, ya kuma zama sabuwar hedikwatar daular Jukunawa zalla, a maimakon daular haɗaka ta Kwararrafa da Jukunawa suka shugabanta wacce ke ƙunshe da mabanbantan yarurruka.

Jama’a:
Tun da fari, garin Wukari an kafa shi ne unguwa-unguwa, wanda kuma kowace unguwa mazauna cikinta kusan zuriya guda ce. Daga cikin irin wannan unguwanni akwai Go-Ndoku, wacce ke nufin gidan sarki ko fadar sarki. Sai kuma wasu unguwannin da suka haɗa da Kinda Kuvyo, Adikyu-Gashi, Ndo Abonta, Kwanse, Ndo-Nwugye, Tsupando, da sauransu (Adamu, 2016).

Gari ne wanda ke kewaye da ganuwa da kuma ƙofofi guda bakwai duk da cewa a yanzu, ƙofar arewa ce kaxai ta saura da jama’a ke amfani da ita; wacce kuma a zamanin baya, mafita ce ta gawarwakin jinin sarauta. Haka nan kuma a tsakiyar garin akwai tsohuwar kasuwar da tun da aka kafa garin take.

Sahun farko na sauran yarurruka mazauna wannan gari na Wukari akwai Gobirawa, waɗanda kasuwanci ya kai su garin kuma suke zaune kusa da fadar sarki, wanda har ta gai ga shugabansu mai suna Maiwuya ya auri ‘yar sarkin Wukari na wancan lokacin abin da ya bashi damar da aka yi masa sarkin kasuwar wukari, wanda ke da alhakin tattara haraji.

Haka nan kuma a shekarar 1932, a zamanin Aku Amadu Agbumanu, wasu jama’a daga Sakkwato sun ƙaura zuwa Wukari, biyowa bayan tuɓe sarkin Musulmi Muhammadu Tambari da aka yi, wanda kuma ya yi gudun hijira zuwa garin na Wukari, inda a can ya rasu kuma aka binne shi a can. A yanzu haka sauran zuriyarsa suna zaune a wannan gari na Wukari a wata unguwa da ake kira Unguwar Sakkwato wacce ke daura da Akata.

Bayan zamowar wannan gari na Wukari helikwatar masarautar Jukunawa, shi ne kuma helikwatar ƙaramar hukumar Wukari a ƙarƙashin jihar Taraba. Yanzu haka wannan gari yana da ci gaban da har ta kai ga yana da jam’o’i guda uku da kuma sauran manya da ƙananan makarantu.

Daga farkon kafa wannan gari zuwa yau, sarakuna ishirin da huɗu ne suka shugabance shi. na farkonsu shi ne Angyu Katakpa (1596 – 1615), sai kuma na ƙarshe wanda har yanzu yake kai (Dr.) Shekarau Angyu Masa-Ibi, Kuvyo II (1976 zuwa yau).

Jukunawa:
Jukun, kalma ce da ke nufin ‘mutum’ a yaren Jukunanci (Okunna da Gausa, 2014), kuma, yare ne da wasu jama’a ke magana da shi. Dukkan wanda ya gaji wannan yare ya zama bajukune, jama’unsu kuma, Jukunawa. Su mutane ne masu karvar baƙi, son zaman lafiya, son jama’a, biyayya, fafutikar ƙwatar ‘yanci, sannan kuma a lokaci guda jarumai a fagen yaƙi (Taraba Online, 2014). Suna yaƙi da duk nau’o’in danniya da zalunci.

Sun kafa daular Kwararrafa tare da haɗin guiwar wasu ƙabilu da suka haɗa da Igala, Ibira Nupe da sauransu. Kwararrafa Daula ce da ta yi yaƙi da wasu daga cikin manyan daulolin ƙasar Hausa kamar irin su Kano, Katsina, Zazzau, da sauransu. Daular da ta ruguje daga baya ta samar da sabuwar daular Jukun Zalla da ke da helikwata a garin Wukarin jihar Taraba.

Asali:
Jukunawa, sun shigo garuruwan baƙaƙe (Bilad Sudan) daga gabas. A tattanawar da muka yi da Martaba Sarkin Pindiga, Alhaji Muhammad Sayoji Ahmad a ranar 13/02/2017, ya shaida mana cewa, Jukunawa sun fito ne daga Yamen, suka shigo ta ƙasar Sudan ta yau, inda suka yada zango a garin Kartum (Khartoum ta Sudan).

Daga nan suka rankayo ta gefen kogin Cadi, kama-kama har suka zo Dutsin Bima. Daga wannan Dutsi na Bima ne suka rabu gida biyu; kashi ɗaya daga ciki suka kama hanyarsu tiryan-tiryan har zuwa Dutsen Binga, inda suka kafa wani gari wanda a yau ake kiransa da sunan Yalwa. Nan suka zauna a kan wannan dutse har zuwa lokacin da sarkin Gombe Umaru Kwairanga ya ci su da yaƙi, abin da ya haifar da tarwatsewar su zuwa wasu sassa na wannan yanki har zuwa kusa da kogin Biniwai a wani yanki da ake kira Pi, wanda daga baya ya zama helikwatar daular Kwararrafa.

Dakta Dawuda (2011), da Mac-Leva (2009), sun ruwaito cewa Jukunawa daga Yemen suka zo. Dr. Dawuda (2011) ya ƙara da cewa, Jukanawa asalin su Yahudawa ne saboda zuwan Yahudawa Nijeriya har garin Wukari, don gudanar da bincike kan ɓaraguzan kayan yaƙi da suke da alaqa da su. Sannan kuma ya jaddada cewa su Jukunawa suna da wani salon rubutun da ya ke kama da Hibiranci (Yaren Yahudu).

Amma (Okunna, Emman, Gausa, da Solomon, 2014; Ujorha, 2012), sun haɗu a kan cewa asalin Jukunawa daga ƙasar Misira (Egypt) suke. Inda a Ujorha (2012), aka nuna cewa akwai kamanceceniyar al’adu da addini da Jukanawan Kona da mutanen Tsohuwar Masar, duk da cewa takardar ta ruwaito tsangayar tarihi ta kwalejin gwamnatin tarayya (Federal College of Education) da ke Jalingo ta danganta asalin nasu da Yamen.

Rabe-Raben Jukunawa:
Gamgum (2015), ya kawo cewa, daga ƙarni na ashirin zuwa yau, Jukunawa sun rarrabu zuwa kashe-kashe kamar haka:

  1. Jukunawan Asali: waɗannan su ne waɗanda ba su da wani yare idan banda Jukunanci; su ne dukkanin wani mutum wanda iyayensa da kakaninsa jukunawa ne sannan kuma ba shida wani yare sai Jukunanci.
  2. Jaukunawan Dole: waɗannan su ne Jukunawan da suna da yaren su na asali wanda ba Jukunanci ba, amma saboda wasu dalilai suka saka su zama Jukunawa. Dolen da ake nufi a nan tana iya zama ta fuskacin yaƙi kamar bayi da ake kamawa lokacin yaƙi ko kuma ‘yan-ci-rani da ke zuwa cikin Jukunawa su zauna har wani lokaci mai tsawo da ka iya sakawa asalin nasu ya ɓace, saboda haka sai su zamo basu da wani harshen-uwa sai Jukunanci. 
  3. Ƙawayen Jukunawa: waɗannan su ne mutanen da su ke da wani gado ta fuskacin yare da al’adu da asali da daula, kuma suka ci gaba da riƙe waɗannan al’adu nasu, amma kuma akwai dangantaka ta ƙut-da-ƙut wacce ka iya zama ta zamantakewa, tattalin arziki, siyasa, addini, ko wani abu dabam, wacce suka ƙulla don cimma wannan manufar tare.  Iri waɗannan Jukunawa sun haɗa har da waɗanda suka yarda su bada jiziya dan kuɓuta daga hare-haren yaƙin abokan gaba na cikin ƙarni na goma sha huɗu. Misali, akwai waɗanda suka nemi tallafin Jukunawa don samun kariya daga hare-haren yaƙuƙuwan Kano, Katsina da Zazzau a cikin shekarun qarni na 14.

A tattaunawar mu da Alhaji Gambo Garba, Galadiman Pindiga a ranar 13 ga Fabrairu, 2017, ya faɗi cewa, Jukunawan asali sun karkasu zuwa:

  1. Jukun Wukari.
  2. Jukun Pindiga.
  3. Jukun Kona.
  4. Jukun Kuteb

Yaƙe-yaƙe:
Jukunawa wanda suka samo asali daga Kwararafa, mutane ne masu matuƙar jarumtaka wajen yaƙi, a binciken da muka gudanar, mun ci karo da cewa, Jukunawa sun yi galaba a yaƙin da suka gwambza da manyan daulolin ƙasar Hausa waɗanda suka haɗa da Kano, Katsina, da kuma Zazzau (Northern Nigerian Publishing Company, 1970; Wikipedia, 2016).

Wannan magana muna iya ƙarfafar ta daga sunayen wasu unguwanni guda biyu da ke cikin garuruwan Kano da Zariya. A garin Kano akwai wata unguwa mai suna ‘Yakasai’, wacce ruwayar kunne-ya-girmi-kaka ta sheda mana cewa kalama ce da ke nufin ‘Za mu dawo ko muna dawowa’ wacce ta fito daga bakin su Jukunawa a lokacin da suka ci Kano da yaƙi. Haka nan kuma akwai unguwa mai suna Tudun Jukun a cikin garin Zariya, wacce ita ma Jukunawa suka kafa ta bayan sun ci garin na Zazzau da yaƙi.

Sarki Ali Mai na Daular Borno, shi ne ya taka musu birki a lokacin da suka kaiwa Ngazargamu harin yaƙi kamar yadda Wikipedia (2016), ta naƙalto a kundin tarihin Katsina (Katsina Chronicle).

Yawan Jama’a:
Duk da ba wani cikakken ƙayadadden adadin yawan Jama’ar Jukunawa, amma dai ana harsashen yawan su ya haura miliyan biyu da rabi (Shishi, 2014). Jukunawa suna zaune cikin garuruwa da dama a  Jihohin Taraba, Binuwai, Nasarawa, Kano, Kaduna, Katsina, Filato, Adamawa, Gombe da sauran wasu garuruwan a wasu Jihohin da yawan su ya kai kusan jahohi 22 a Nijeriya da kuma wani yanki na arewacin-yamman ƙasar Kamaru (North western Cameroon).

Al’adu:
Daga cikin manya-manyan al’adun Jukunawa, akwai al’ada mai suna Ukenho, wacce ake gudanar da ita a qarshen shekara, sannan kuma akwai Ungu da sauransu.