Ruwan Jiki (3)

Daga MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI

’Yan uwa masu karatu Assalamu alaikum. Barkanmu da wannan lokaci, barkan mu da sake saduwa a wannan shafi mai ilmintarwa, da ke zayyano muku bayanai game da duniyar jikin ɗan adam, domin ku fa’idantu kuma ku ilmintu, kuma ku san yadda Jikinku ke aiki.

Har yanzu dai muna magana akan ruwan jikin ɗan Adam. A satikan da suka gabata, na kawo yadda ruwa yake a jikin mutum, guraren da ake samun sa, da muhimman ayyukansa da tasirinsa a jikin bil adama. 

Na faɗa cewa: Ruwan jikin ɗan Adam cibiya ce ta musayar sinadarai, saƙonni, da kuma sufurin narkakkun abubuwa irinsu abinci, magunguna, da sinadarai kala-kala. Duk wani abu da zai taɓa ruwan jiki ashe zai taɓa waɗannan abubuwa da lissafa! muhimmancin ruwan jikin ɗan Adam ya kai ƙadarin da idan yayi ƙaranci, to rashin lafiya za ta iya afkuwa.

Ina ga ya kamata a wannan satin in ɗan yi bayani game da abubuwan da kan je su zo yayin da ruwan jikin ɗan Adam yayi ƙaranci, sawa’un gaba ɗaya ruwan jikin ne yayi ƙaranci ko kuwa wani ruwa ne da ke keɓantaccen sashe yayi ƙaranci.

Amma kafin nan, akwai buƙatar na faɗi wannan: jilin ɗan adam ya fi rasa ruwa yayin lokacin zafi fiye da lokacin sanyi. Ko me ya sa hakan? Dalili shi ne; a tsari na jiki, kullum cikin aiki yake. Kuma mafi yawancin aikin da jiki zai gudanar, ya na fitar da zafi. Kamar dai kai ne ka kunna akwatin talbijin. Bayan wasu lokuta tana kunne, idan ka taɓa ta za ka ji tayi ɗumi. To shima haka jiki ya ke. Da fatan an gane. Wannan kenan. To, tun da jiki ya na samar da zafi a kowanne lokaci da mutum yake raya, ya kake tunani a ce ga zafin jiki, ga kuma zafin yanayi?

Hikima ce ta Sarkin halitta Ya ƙaddara cewa jikin mutum zai dinga ƙoƙarin rage zafin da ke ciki, a lokacin da xan Adam ya tsinci kansa a yanayi na zafi. Ɗaya daga cikin hanyoyin ita ce fitar zuffa daga jiki. To tun da shi gumi ruwa ne, idan mutum ya rasa shi, ya rasa sashe na ruwan jikinsa ko jikinta kenan. Saboda haka lokacin zafi muna rasa ruwan jiki ta hanyar gumi. Amma ruwan da muke rasawa ta hanyar fitsari yana da yawa matuƙa! A lokacin zafi, ruwan da yake fita ta fitsari mai yawa ne kuma surkakke ne. Ma’ana babu sinadarai da yawa a ciki.

A lokacin sanyi kuwa, yunqurin jikin ɗan Adam shi ne ya adana ruwan jiki da yake da shi a wannan yanayi. Shi yasa fitsari da ake yi lokacin sanyi ba shi da yawa, juma cike ya ke da sinadarai. Idan da zaka kalli kalarsa, za ka ga yayi ruwan rawaya sosai saboda yawan sinadaran da ke cikinsa. Idan dace sinadarai a wannan gava, ina nufin sinadaran da jiki ya gama amfani da su. Kuma dama hanyoyin da jiki ke fitar da abubuwa marasa amfani su ne: bayan gari, zuffa, da fitsari. 

Ruwan jikin ɗan Adam baya qaranci saboda ruwan da ya fita ta hanyar fitsari. Dalili kuwa shi ne saboda shi za a maye gurbin ruwan da aka rasa ta hanyar shan ruwa, da kuma cin abinci. Sannan kuma abisa tsarin aikin jikin ɗan Adam, idan ruwa ya yi yawa shima ana rage shi ta hanyar fitsari. Wannan shi muke kira da “water balance” a turance. 

Muna rasa ruwa ta hanyar gumi, fitsari, bayan gida, numfashi, da magana. Amma wasu masana suna ganin cewa ruwan da muke rasawa ta hanyoyi guda biyun ƙarshe wato: numfashi da magana, ba su taka kara sun karya ba. Amma dai idan aka haɗa su cikin lissafo, su ma su na bayar da tasu gudunmawar wajen rasa ruwan jiki.

Ɗaya daga cikin hanyoyin da muke rasa ruwa daga jiki, ita ce hanyar motsa jiki. A lokacin motsa jiki, ƙwayoyin halittun jiki musamman na tsoka da hanyoyin jini kan ƙara yawan ayyukansu domin bawa tsoka dama ta mommotsa. Yawan fitar gumi yayin motsa jiki shi ne sanadiyyar rasa ruwan da ke faruwa. 

Ɗan Adam zai iya rasa ruwan jiki yayin da ya rasa jini. Babban misalin da zan baku domin ku gane, shi ne rasa jini ta hanyar haɗari, ko kuma mace ta rasa jini yayin haihuwa. A wannan yanayi, jikin ɗan zai bi hanyoyi wajen maye gurbin ruwan jikin da a ka rasa, misali ta hanyar kunna cibiyar samar da ƙishirwa. Yayin da ƙishirwa ta samu, to ɗan Adam zai nemi ruwa ya sha, hakan zai sa fara maye gurbin ruwan da a ka rasa. Amma kam ƙwayoyin jininsa a ka rasa a lokacin haihuwar ko a lokacin haɗarin kan ɗauki tsawon lokaci, kimanin sati shida.

Haka kuma ɗan Adam kan rasa ruwan jiki yayin da ya samu ƙuna. A ilimin likitanci, an sanya ƙuna kashi uku. Kowacce da irin ta’annatin da ta ke yi a jiki. Amma kuma duka ukun kan kawo ƙarancin ruwan jiki.
Ƙuna mai mataki na farko ita ce wadda ta cinye iya fatar jiki, ba tare da taɓa sauran halittun da ke maƙwabtaka da ita ba (wato halittunnda ke ƙarƙashinta). 

A duk lokacin da ruwan jikin yayi ƙaranci saboda motsa jiki mai tsanani, rasa jini, ƙuna, yawan gumi da sauransu, hakan kan nuna alamu da ke nuna cewa lallai ruwa ya yi ƙasa. Misali: qishirwa, rashin ƙarfi da kuzarin jiki, bushewar baki, faɗawar idanu, yin fitsari mai tsananin zarni, da sauransu. 

Haƙiƙa mutum zai saurin rasa ruwan jiki idan ya daɗe a rana, ko idan ya na da ciwon sukari, ko idan yayi amai ko gudawa, ko kuma idan ya sha magani mai sanya yawan fitsari misali maganin hawan jini, ko kuma shan giya shima ya ka sa ruwan jiki ya ragu. Ajin mutanen da ke cikin haɗarin samun qarancin ruwa a jiki su haɗar da tsofaffi, Jarirai, mashaya giya, da kuma masu daɗaɗɗen ciwon sukari.

Na San yanzu mun fahimci cewa ruwa jiki na da matuƙar tasiri da muhimmanci a jikin ɗan Adam. Saboda haka ina jan hankalinmu da mu dinga kula da shan ruwa. Ko da ba mu ji qishi ba. Rashin shan wadataccen ruwa kan kai mutum ga ciwon kai, rashin ƙarfin jiki, ko basir (bayan gari ya dinga tauri), da sauransu. 

Masu karatu ku tara a sati mai zuwa domin ci gaba da kawo muku bayanai akan jikin ɗan Adam. Kafin nan na ke cewa Assalamu alaikum.