Ilimin ‘ya’yan Fulani na da muhimmanci a wannan zamani – Hauwa Umar Aliyu

Daga ABUBAKAR TAHEER a Haɗeja

Mai karatu wannan tattaunawa ce ta musamman da Hauwa Umar Aliyu, matar da ta fito daga rugar Fulani, kuma mai taimakon mata da marasa galihu. Ta fito daga garin Birniwa na Jihar Jigawa. Ta yi gidauniya mai suna Iya Hauwa Foundation. A sha karatu lafiya:

MANHAJ: Mu fara da jin tarihinki a taƙace

Sunana Hauwa Umar Aliyu. ‘Yar Ƙaramar Hukumar Birniwa ce a Jihar Jigawa. Ni Bafilatana ce daga riga, saboda ban ma iya Hausa ba a lokacin da yayar Mahaifina da ke zaune a Kano ta ɗauke ni ta tafi da ni Kanon.

Kafin a kawoni Kano, na fara karatun addini gaban mahaifiyata a nan rigamu, na yi karatuna tun daga firamare har zuwa Jami’a inda na yi digirina na farko a ɓangaren ‘Education Islamic Studies’ a garin Kano.

Bayan kammala karatu, na yi bautar ƙasa a kano, daga nan na fara aikin koyarwa. Na fara aikace-aikace na aikin sa-kai na ƙungiyoyi, daga ciki na samu damar zama daraktan tsare-tsare ta ƙungiyar miyatti a jiharmu ta Jigawa.

A ɓangaren karatu, bayan digirina na farko, na je Kenya, na yi ‘Postgraduate Diploma a ɓangaren lafiyar mutanen Karkara (Community Health) da na gama na dawo gida, na ci gaba da aiki wanda ya haɗa da aiki da ƙungiyoyi na ƙasashen waje, sai kuma na sake komawa karatu. Na sake yin ‘Postgraduate Diploma in Education’, a ‘Health Promotion’ a University College London (UCL) da ke Ƙasar Biritaniya (UK). Na kuma yi ‘masters ɗina (Msc) akan Muradun-ƙarni da ake yi musu laƙabi da ‘Sustainable Development Goals’ (SDGs) a Jami’ar Sussex da ke Brighton a ƙasar Ingila (UK).

Yaushe ki ka buɗe gidauniyarki ta Iya Hauwa?
Dama kamar yadda na gaya maka a baya, ina cikin ayyuka kala-kala da suka shafi al’umma. To ita Gidauniyar Iya Hauwa an yi mata ‘register’ da CAC a shekarar 2016. Dalilin buɗe wannan gidauniya shine; ci gaba da tallafa wa al’ummar mu na karkara da rigage domin inganta da kyautata rayuwarsu a harkar lafiya, yaƙi da talauci, ilimin ‘ya’yansu da sauran duk abubuwa da suka shafi rayuwa waɗanda muradun-ƙarni (SDGs) ke ƙoƙarin ƙarfafawa. 
Mu na bawa ilimi muhimmanci ƙwarai da gaske a faɗakarwar da mu ke yi wa al’ummar mu, saboda ni na san daɗin ilimin tunda na fito daga riga, na samu na yi karatu har zuwa Ingila (UK), kuma na samu dama masu yawa ta hanyar wannan ilimin da na samu. 

Kin yi aiki da ƙungiyoyi ne ko gwamnati?
Eh, na yi ayyuka da dama daga koyarwa a aji, zuwa aiki da ƙungiyoyi na gida (a cikin ƙasarmu Nijeriya) da ƙungiyoyi na ƙasashen waje. Aikina na ƙarshe da nayi shine mai taimakawa gwamna a ɓangaren Mata (Special Assistant on Women Empowerment), na yi aiki da Mai girma Gwamna Alhaji Badaru Abubakar (MNI)

Waɗanne ayyuka wannan gidauniya ta Iya foundation take gudanarwa?
Babban aikinmu shine tallafa wa mata da marasa galihu, sannan kuma muna ƙarfafawa wajen ilimantar da ‘ya’yanmu dake karkara musamman yaranmu Fulani. Mukan dage wajen faɗakarwa, don ganin yaran da suke karkara musamman waɗanda suka fito daga riga sun samu ilimi.

A tallafin da muke bawa mata, mukan haɗa musu da bishiya domin su dasa, kuma su lura da ita, domin yaƙi da hamada. A wannan tallafi da mu ke yi mu na haɗawa da matasa, su ma mu na ba su bishiya, kuma muna ba su sharaɗi na lallai su koma makaranta ko ta boko ce ko ta Muhammadiyya.

Wane ƙalubale ku ke fuskanta?
Babbar matsalar da muke fama da ita shine rashin kuɗi, domin yin ayyukan mu da muka sa a gaba. Annobar Korona ta taimaka wajen matsalar rashin kuɗi, saboda duk abubuwa sun tsaya cak.

Waɗanne nasarori wannan gidauniya ta samu?
Mun samu nasarar farfaɗo da wata makaranta a wani mauye (Fajiganari) a nan Birniwa, sannan mu kan ɗauki masu koyar da su karatu musamman waɗanda suka kammala NCE, mu na ba su ɗan tallafi duk wata. A yanzu haka muna ƙoƙarin buɗe ‘Nursery School’ a nan Birniwa. Haka zalika mu kan bada tallafi ga ɗalibai wajen biyan kuɗin makaranta da kuma siyan fom na JAMB.

Wacce shawara ki ke bawa matasa da suka yi karatu don neman na kansu?
Gaskiya kira na gare su shine, a dage wajen koyon sana’o’i, kar mutum ya dogara da yayi karatu, mu dage mu nema wa kanmu ‘yanci, mu cire ƙangin talauci. Haka kuma matasa su rinƙa neman irin waɗannan ƙungiyoyi namu suyi ‘joining’ suna ba da tasu gudunmawa.

Mun gode.
Na gode Kwarai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *