Baya ta haihu kan batun sakin ɗaliban Yawuri

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Ranar Larabar da ta gabata ne labarin sako ɗaliban makarantar Birnin Yauri (Yawuri) ya mamaye kafafen yaɗa labarai bayan da wani ya aika labarin ta yanar gizo, inda ya rubuta kamar haka; “Kimanin ɗalibai da ma’aikata sama da 90 da aka sace a Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Yawuri a Jihar Kebbi sun shaqi iskar ‘yanci bayan kwanaki 118.

Rahotanni daga jihar sun bayyana cewa, mahaifin ɗaya daga cikin ɗaliban da aka kama, wanda bai so a ambaci sunansa, shine ya tabbatarwa da Daily Trust hakan a daren nan, kamar yadda jaridar ta wallafa a shafinta.”

Wannan maganar ta saka mutane murna ba kaɗan ba tun kama daga ’yan uwan da abokan dangin ɗaliban da kuma malamansu, sai maganar daga qarshe tana neman ta zama ƙanzon kurege, saboda Wakilin Manhaja ya zanta da mutane da yawa a garin na Yauri, inda hasali ma waɗansu su kan ce yanzu ne suke samun wannan labari daga gare shi. Hakan ya nuna cewa, baya ta haihu kenan.

Wakilin Manhaja ya zanta da Malama Aina’u mai shekaru 37, wacce yaranta uku aka sace sai dai ta ce ɗayan yana cikin yaran da suka kuɓuta kwanakin baya daga Zamfara, ta bayyana cewa su kamar arba’in ne daga garuruwan Koko da Zuru da Yauri da sauran garuruwa suka garzaya gidan gwamanti bayan jin an ce an gwamna ya sanar da cewa an sako yaran kuma suna kan hanyar su ta zuwa Kebbi daga Abuja amma da suka zo gidan gwamanti sai jikinsu ya mutu saboda ba su ga wata alama ta walwala ba da ke nuna gaskiyar al’amarin.

An dai bayyana musu da cewa gwamnan ba ya gari saboda haka ba wani wanda zai iya yi musu wani bayani saboda haka sai suka koma jiki a mace.

Ta ce, ita tana daga cikin waɗanda suka ga tashin hankalin da idonsu, saboda a gabanta aka sace ɗaliban kuma su ɗari da talatin da biyar ne aka sace ba kamar yadda ake cewa ba wai ɗari da hamsin waɗansu su ce casa’in sannan kuma ta nemi hukuma da ta gaya musu gaskiyar al’amari idan an kashe yaransu shikenan sai su haqura amma yanzu a kullum cikin jimamin wane hali yaransu suke ciki ya mamaye zukatansu wanda yanzu haka ta san mutane musamman mata, ‘ya’ya ɗaya-ɗaya da suka rasu sanadiyyar rasa yaran nasu.

Ta kuma bayyana cewa, yaran idan ma suna raye, to suna cikin dajin Zamfara, kamar yadda yaronta da ya kuvuto ya bayyana.

Alhaji Sani Abacha, wani ɗan kasuwa da yake zaune a garin na Yauri kuma ɗan uwa ne ga wani da aka sace ɗansa, ya ce, shi ma wani abokinsa da ke aiki a Majalisar Sarkin Gwandu ne ya kira shi ya ke tambayar sa inda shi kuma ya amsa masa da cewa ba shi da labari, amma ku da ku ke Hedikwata ai ku me ya kamata a sami wannan labarin wajenku.

Ya qara da cewa, magana ta gaskiya babu wani labari mai kama da wannan saboda akwai wani ɗan uwansa da aka tafi da yaronsa kuma har yanzu ba labarinsa.

Mataimakin Shugaban makarantar ta Birnin Yauri Malam Mukhtari Abdullahi Gulma wanda shi ma yana daga cikin malaman da aka tafi da su, wakilinmu ya zanta da kaninsa Malam Ibrahim Abdullahi Gulma inda ya bayyana cewa magana ta gaskiya har yanzu babu takamaiman gaskiyar magana saboda duk inda muka tuntubi wata hukuma ba wani bayani mai ƙarfafa muna gwiwa, saboda haka mu ke ganin wannan maganar ƙanzon Kurege ce kawai sai dai a ko da yaushe fatar mu Allah ya dawo muna da su lafiya.

Mai baiwa gwamna shawara kan harkar tsaro Garba Rabi’u Kamba ya fito a kafafen yaɗa labarai ya bayyana cewa, har yanzu dai magana ta gaskiya babu wata magana da ta zo wajensu a hukumance dangane waɗannan ɗaliban da malaman su da aka sace, idan ma dai an samo su to ba su zo hannunsu ba.

Gwamnatin ta Kebbi dai ta yi ƙaurin suna wajen kaulin-la-amalin saboda a kullum sabon shafi ta ke buɗewa dangane da sace waɗannan ɗaliban inda a baya har ta yi kurarin shiga jeji don farauto waɗannan yaran amma daga baya kuma maganar ta zama maganar teburin mai shayi wanda har mafarauta da ‘yan tauri da aka shirya su ma suka gano ana yaudarar su ne saboda haka sai auka kwance damarar da suka yi kowa ya kama gabansa.