Shin Gwamna Ganduje ya tsokano tsuliyar dodo?

*Malaman Kano sun yi wancakali da shirin gwamnatinsa na tuge jagoransu
*Sanatocin jihar sun yi masa tawaye

Daga HAMISU IBRAHIM da AMINA YUSUF ALI a Kano

Siyasar Jihar Kano tana da wuyar sha’ani ta fuskar tarihi, inda a mafi yawan lokuta wasu ɓangarori kan zamo silar rugujewar tafiyar ɗan siyasa bisa la’akari da waɗanda suka yi masa taron dangi. Ire-iren waɗannan vangarori sun haɗa da malamai, sarakuna da kuma gidajen siyasar jihar. Ba kasafai wani ɗan siyasa kan yi galaba kan waɗannan sassa ba ko da kuwa shi ke riƙe da madafun ikon jihar a matsayin gwamna.

A cikin wannan makon za a iya cewa, Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya shata daga ɓangarorin siyasar jihar da kuma na malamai, inda Haɗakar Majalisar Malaman Jihar Kano suka yi wancakali da yunƙurin da ake zargin wasu hadiman gwamnan sun shirya na tunɓuke Shugaban Majalisar Malaman Jihar, Sheikh Ibrahim Khalil. Haka nan a cikin makon dai, ɗaukacin sanatocin da ke wakiltar jihar a Majalisar Dattawa ta Ƙasa sun barranta da gwamnan, inda suka fito suka yi tawaye ga salon mulkinsa. Da ma kuma babu abin da ya sauya kan adawar da ke tsakaninsa na tsohon Gwamnan Jihar kuma jagoran babbar adawar jam’iyya a jihar (PDP), wato Dr. Rabiu Musa Kwankwaso.

A cikin wata sanarwa mai ɗauke da goyon bayan mafi yawan jagororin ɗariƙun jihar, Zauren Haɗin Kan Malamai da Ƙungiyoyin Musulunci na Jihar Kano ya nesanta kansa da wata sanarwa da ya ce wasu mutane sun bayar game da sauke Sheikh Ibrahim Khalil daga matsayin shugabancin Majalisar Malamai ta Ƙasa reshen jihar Kano tare da ayyana wanda suke sha’awar ya shugabance ta. Jagororin wannan zaure sun ce sam wannan mataki ba da yawunsu aka zartar da shi ba.

Sanarwar da jagororin zauren suka fitar wadda ta sami sa hannun sakataren zauren, Dr. Saidu Ahmad Dukawa, kuma mai ɗauke da kwanan wata 12 ga Oktoba, ta ce, “Jagorancin Zauren Haɗin Kan Malamai da Ƙungiyoyin Musulunci na Jihar Kano sun samu labarin wata sanarwa da waɗansu mutane suka bayar suna masu iƙirarin sauke Sheik Ibrahim Khalil daga shugabancin Majalisar Malamai ta Ƙasa reshen jihar Kano, tare da ayyana wanda suke sha’awar ya shugabance ta.

“Jagororin suna masu tabbatar wa al’umma cewa ba da yawunsu aka yi wannan jawabi ba kuma ba sa goyon bayansa. Har kullum jagororin suna neman zaman lafiya ne da haɗin kan arumma, amman wannan yunƙurin zal haifar da saɓanin haka ne.

“Don haka Zaure yana kira ga alumma da su ci gaba da ririta zaman lafiyar Kano su guji duk wani abu da zai iya zama barazana ga tsaro da kwanciyar hankali.

“Jagororin da suka amince da a fitar da wannan sanarwa su ne Farfesa Musa Muhammad Borodo, Khalifa Sheik Ƙaribullah Sheik Nasiru Kabara, Sheik Abdulwahhab Abdallah, Sheikh Ibrahim Shehu Maihula, Farfesa Muhammad Babangida Muhammad, Dr. Bashir Aliyu Umar, Imam Nasir Muhammad Adam da Dr. Ibrahim Mu’azam Maibushira.”

Wata majiya ta tabbatar wa da Manhaja cewa, Mai Bai Wa Gwamnan Jihar Kano Shawara kan Harkokin Addini, Hon. Ali Baba Agama-Lafiya, da wani hadimin gwamnan mai suna Ba-Kwana na daga cikin waɗanda suka ɗauki nauyin sanarwar da aka fara bayarwa ta sauke Shugaban Majalisar Malaman a wani taron manema labarai a Birnin Kano.

To, amma Kwamishinan Yaxa Labarai na Jihar, Kwamred Muhammad Garba, ya ƙaryata wannan zargi, inda ya ce, gwamnatin Kano ba ta da hannu a wannan sanarwa lokacin da ya zanta da kafafen yaɗa labarai a jihar.

Ana cikin wannan badaqalar siyasar ne kuma, sai a ranar Larabar da ta gabata ne, Sanatoci masu wakiltar Jahar Kano tare da takwarorinsu na majalisar dokoki ta tarayya suka hallara a Birnin Tarayyar Abuja, don tattaunawa a kan abinda ya daɗe yana ci musu ƙwarya wato irin kamun ludayin Gwamna Ganduje a kujerar mulkinsa da kuma yadda ya ɗauki jam’iyyar kacokan ya mayar da ita tasa shi kaɗai yana yadda ya ke so. 

Mahalartan wannan taron sun haɗa da Sanata Malam Ibrahim Shekarau da Sanata Barau Jibril. Daga ɓangaren ‘yan majalisa kuwa akwai Hon. Sha’aban Sharada, wanda da ma suka daɗe suna sa-toka, sa-katsi tare da Gwamnan tun bayan zaɓen sa a matsayin ɗan Majalisa a shekarar 2019.

Kwana ɗaya bayan kammala taron ne suka fitar da wata sanarwa a jiya su na masu bayyana matsayarsu kan kama karya da suka ce an tafka a zavukan ƙananan hukumomi da mazaɓun jihar na jam’iyyar, inda suka aike wa shugaban jam’iyyar na ƙasa takardar ƙorafinsu.

A cikin abubuwan da suka tattauna a zaman da suka yi sun haɗa da yadda za a samar da ɗan takarar Gwamnan Kano na Jam’iyyar APC a kakar zaɓe mai zuwa da kuma rashin amincewarsu ga yadda uwargidan gwamnan ta ɗaga hannun Murtala Garo a matsayin wanda jam’iyyar za ta yi, da kuma yadda gwamnan ya ke haɗa gwarama a tsakanin masu riƙe da muƙami da kuma al’ummar jihar Kano. 

Haka nan, an rawaito cewa, sun nuna bara’a da rashin goyon bayansu ga shugaban riƙon ƙwarya na Jihar Kano, mai ci yanzu, Alhaji Abdullahi Abbas, inda suka yanke shawarar a tumɓuke shi, don a nemi wani a ɗora, domin ‘yan jam’iyyar da dama ba sa jin daɗin mulkin nasa.

Game da wannan taro na Abuja, Shugaban Ƙaramar Hukumar Birnin Kano da Kewaye, Hon. Fa’izu Alfindiki, ya bayyana cewa, ɗaya daga cikin sanatocin kuma tsohon gwamna, Sanata Kabiru Gaya, ya nesanta kansa da wancan tawayen da aka ce an yi.

Ko babu komai dai masu nazari na kallon wannan tashin-tashinar siyasa a matsayin wata hanya ta karya lagon siyasar gwamnan, domin hakan na nuni da cewa, jiga-jigan siyasar jihar ba su tare da tafiyar gwamnan, inda hakan na iya kawo masa tazgaro a 2023.