Dokar aika sakamakon zaɓe: Akwai buƙatar jituwa tsakanin majalisa da INEC – Atiku

Daga MAHDI M. MUHAMAD a Abuja

Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a babban zaɓen 2019, Atiku Abubakar ya yaba da yadda aka warware rashin jituwa tsakanin majalisar ƙasa da hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) kan watsa sakamakon zaɓe ta hanyar Intanet.

Wata sanarwa da ofishin yaɗa labarai na tsohon Mataimakin Shugaban ƙasar ya fitar ranar Talata, ya ce, daidaita matsayin tsakanin cibiyoyin biyu wata manuniya ce cewa dimokuraɗiyyar Nijeriya na ci gaba da samun ƙarfi.

Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasar ya kuma yaba wa ɗaiɗaiku da ƙungiyoyi musamman ƙungiyoyi daban-daban masu fafutukar kare dimokuraɗiyya waɗanda suka halarci tattaunawar jama’a kan bayutuwa masu muhimmmanci, inda ya ce, “ta wannan sakamakon, na gamsu cewa cibiyoyin gwamnati a Nijeriya za su ci gaba da yin ayyukansu masu kula da manufofin jama’a.”

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “ƙungiyoyin farar hula sune masu lura da manufofin gwamnati da cibiyoyi. Ba don da jajircewar ƙungiyoyin farar hula ba, da ba mu zo wannan tafarkin ba. Wannan sakamakon ya kamata ya ƙara ƙarfafa gwiwar ‘yan Nijeriya da ƙungiyoyin farar hula da su ƙara himma don tabbatar da kyakkyawan shugabanci a ƙasar.”