Daga CMG HAUSA
Wasu mintuna 5 da suka wuce, na yi kai-komo tsakanin wasu nau’o’in waken gahawa na Kenya, da Habasha, da Rwanda, kafin na zaɓi ɗaya daga cikin su, na zabi waken da aka samar da shi daga yankin Muranga na ƙasar Kenya, don ya zama kyautar ƙaramar sallah, da zan ba kaina.
Na sayi waken ne ta wani dandalin sayar da kayayyaki ta yanar gizo na ƙasar Sin. A kwanakin nan, ana gudanar da “bikin sayar da ingantattun kayayyakin ƙasashen Afirka” a dandali daban daban na ƙasar Sin. Kawai na danna wani link da ya bayyana a wayar salula ta, sai na ga hoton bidiyon yadda wasu ‘yan Afirka, da Sinawa suke kokarin gabatar da wasu nagartattun kayayyakin Afirka cikin himma: Miyar yaji ta Rwanda, da lu’u-lu’un ƙasar Tanzania, da man koko na Ghana, da darduman ƙasar Morocco, da dai sauransu. Kusan ana iya samun kayayyakin dukkan sassan nahiyar Afirka a wajen wannan biki.
Wataƙila za ku so ku yi tambaya: Me ya sa Sinawa ke son kafa wani bikin musamman ma domin su riƙa sayen kayayyakin ƙasashen Afirka?
Da farko dai, sun yi haka ne don cika alƙawarin da suka yi. A wajen taron ministoci na dandalin haɗin gwiwar Sin da Afirka da ya gudana a bara, inda shugaban ƙasar Sin ya gabatar da manyan ayyuka guda 9 game da haɗin kan Sin da Afirka, ciki har da haɓaka haɗin gwiwar ɓangarorin 2 ta fuskar tattalin arziki mai alaƙa da fasahohin zamani, da ta kasuwanci.
Yanzu, ta hanyar gudanar da wannan biki na sayar da kayayyakin Afirka, an daidaita fasahohi tsakanin dandalin kasuwanci na ƙasashen Afirka da na Sin, da haɓaka ciniki a tsakaninsu. Hakan ya dace da burin Sin na aiwatar da “manyan ayyuka 9” da ta gabatar.

Na biyu shi ne, kawar da shingaye, ta yadda tsarin samar da kayayyaki zai gudana yadda ake buƙata a duniya. Kasancewar wani muhimmin ɓangare na tsarin samar da kayayyakin masana’antu na duniya, ƙasar Sin ba ta son ganin annobar COVID-19, da wutar yaki, da jajayya a fannin siyasa sun zama shingayen da suka hana zirga-zirgar kayayyakin da ake buƙata a kasuwannin duniya.
Saboda haka ƙasar na ƙoƙarin buɗe ƙofarta, da hadin gwiwa da sauran ƙasashe, don tabbatar da gudanar da tsarin samar da kayayyaki, tare da ba kasuwannin ƙasa da ƙasa cikin wani yanayi mai kyau.
Ban da haka, wannan biki na sayar da kayayyakin ƙasashen Afirka ya nuna babban burin ƙasar Sin, yayin da take hulda tare da sauran ƙasashe, wato tabbatar da moriyar juna. Sinawa sun san cewa, manufar barin wani ɓangare ya ci riba shi kadai, yayin da ɓangare na daban ke yin hasara, tana haifar da rikici ne kawai. Kana yunƙurin tabbatar da moriyar juna shi ne tushen zaman lafiya, da haɗin kai, da kuma ci gaba.
Wannan ra’ayi ya sa ƙasar Sin buɗe kofarta, ta hanyar bikin sayar da kayayyakin Afirka, da bikin baje kolin kayayyakin ƙetare, da dai makamantansu, inda take gayyatar ‘yan kasuwan ƙasashe daban daban su zo ƙasar Sin su sayar da kayayyakinsu.
Ta wannan hanya, ‘yan kasuwan ƙasashen waje sun samu riba, kasar Sin ita ma ta janyo jarin waje, da haɓaka ciniki, da kulla hulɗar haɗin kai, gami da ciyar da tattalin arzikinta gaba. Burin tabbatar da moriyar juna ya cika ke nan.
Abokaina, ko kuna da wani kayan da kuke son sayar da su a ƙasar Sin? A hanzarta a fara ɗaukar mataki, don Sinawa na maraba da zuwanku.
Fassarawa: Bello Wang