Me ya sa ake rububin zuba jari a kasuwannin Sin duk da fama da annoba?

Daga CMG HAUSA

Masu hikimar magana na cewa, “ba a fafe gora a ranar tafiya,” kuma a wani ƙaulin akan ce, “tun ran gini ran zane.”

Duk da irin yadda ake fama da yaɗuwar annobar COVID-19 a wasu daga cikin yankuna da biranen ƙasar Sin, ciki, har da ɗaya daga cikin manyan biranen kasuwancin ƙasar wato Shanghai, amma wani abin ban sha’awa shine, yadda ake ƙara samun masu sha’awar zuba jari dake ƙara rububin juba jarinsu a ƙasar.

Alal misali, kamar yadda wani kwararren masanin harkokin kuɗi da aikin banki na ƙasar Swissland, Fiorenzo Manganiello ya bayyana cewa, kyakkyawar makomar da tattalin arzikin ƙasar Sin ke da shi, da yanayin ƙarfin tattalin arzikin ƙasar, da kuma manyan matakan bunƙasa tattalin arziki na dogon lokaci da ƙasar Sin ta ɗauka, sun kasance a matsayin tushen dake kara janyo hankullan masu zuba jari a ƙasar.

Koda yake, ba iya masanin bankin ne kaɗai ke da irin wannan ra’ayi ba, ita ma jaridar British Financial Times ta ƙasar Birtaniya ta bada rahoton cewa, bankunan zuba jari na ƙasa da ƙasa masu yawan gaske, suna ƙara nuna sha’awarsu na shirin fadada hulɗar kasuwanci da birnin Shanghai, kuma halin da ake ciki game da matakan yaki da annobar COVID-19 da aka ɗauka a birnin ba su kashe gwiwar masu son zuba jarin ba.

A cewar Manganiello, wanda shine mamallakin kamfanin Lian Group, wani kwararren kamfanin zuba jari a Turai, yace shirye-shiryen faɗaɗa kasuwancin ya nuna cewa, ƙasar Sin ta kasance a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashen duniya da tattalin arzikinta yake da ƙarfin gaske a lokacin da ake fama da annoba, kuma makomar bunƙasuwar tattalin arzikin tana da matuƙar ƙarfi fiye da mafi yawan ƙasashe mafiya ƙarfin tattalin arziki a duniya.

Dama dai masana da dama sun yi tsokacin cewa, yanayin tattalin arzikin ƙasar Sin yana cigaba da inganta, kuma buƙatun da ake dasu na kayayyaki ƙirar ƙasar Sin a cikin gidan kasar har ma da ƙasa da ƙasa yana cigaba da karuwa. Haƙiƙa, ƙasar Sin tana jurewa dukkan wahalhalu da haɗɗura, kuma tana da kwarin gwiwar daidaita yanayin manyan ɓangarorin tattalin arzikinta.

Fassarawa: Ahmad Fagam

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *