Da Ɗumi-ɗumi: Diri ya sha rantsuwar zama Gwamnan Bayelsa wa’adi na biyu

Daga BASHIR ISAH

An rantsar da Douye Diri a matsayin Gwamnan Jihar Bayelsa karo na biyu.

Gwamna Diri ya sha rantuwar kama wa’adi na biyun ne ta hannun Babban Alkalin Jihar, Mai Shari’a Matilda Ayemieye da misalin karfe 2 na rana a ranar Laraba.

 Tun da fari sai da aka rantsar da Mataimakin Gwamna, Lawrence Ewhrudjakpo, kafin daga bisani Gwamna Diri ya sha tasa rantsuwar.