Dalilin da ya kai tsohon gwamnan Bayelsa, Sanata Dickson ofishin EFCC

Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin Zagon Ƙasa da Zambar Kuɗaɗe (EFCC) tana riƙe da tsohon gwamnan Jihar Bayelsa kuma sanata mai wakiltar Bayelsa ta Yamma a Majalisar Dattawa, Seriake Dickson.

Wannan na zuwa ne biyo bayan gayyatar da EFCC ta yi wa tsohon gwamnan kan batun da ya shafi zargin aikata ba daidai ba da ofishinsa da kuma sarrafa kuɗaɗen gwamnati ba bisa ƙa’ida ba a shekara takwas da ya yi riƙe da jihar a matsayin gwamana, daga 2012 zuwa 2020.

Da misalin ƙarfe 11 na safiyar yau Dickson ya isa ofishin EFCC da ke Jabi a Abuja, don amsa wa hukumar tambayoyin da ta shirya masa a kan zarge-zargen da aka yi masa.

Ya zuwa haɗa wannan labari, MANHAJA ta fahimci EFCC ba ta rabu da tsohon gwamnan ba.

Mai magana da yawun tsohon gwamnan, Wilson Uwujaren, ya tabbatar da gayyatar da EFCC ta yi wa maigidansa.