PSG ta yi babban kamu

A halin da ake ciki, ya tabbata cewa fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa, Lionel Messi, ya zama ɗan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta PSG.

Ƙungiyar PSG ta sanar cewar Lionel Messi ya sanya hannu a kwangilar shekaru biyu bayan barin sa ƙungiyar Barcelona inda ya shafe shekara 21 yana buga mata wasa.

Sanarwar PSG ta nuna kwangilar ta kuma ƙunshi buƙatar ƙarin shekara guda bayan kammala shekaru biyun da aka cim ma yarjejeniya idan hali ya yi.

Haka nan, cewa Messi zai sanya riga mai ɗauke da lamba 30, lambar da ya yi amfani da ita lokacin da ya fara yi wa Barcelona wasa a shekarar 2004 zuwa 2006.