Gombe PDP: Garry da Mailantarki sun ƙalubalanci shigar Pantami sabon zaɓen fidda gwani

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe

’Yan takarar neman kujerar gwamnan Jihar Gombe a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, Usman Aliyu Garry da Khamisu Ahmed Mailantarki, sun nuna adawarsu da shigar Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami cikin sabon zaɓen fidda gwani da jam’iyyar za ta gudanar ranar Talata.

Matsayar ’yan takarar ta biyo bayan hukuncin babbar kotun tarayya da ke Gombe, wadda ta soke zaɓen fidda gwani na baya da ya samar da Pantami a matsayin ɗan takarar PDP na gwamna, tare da umartar jam’iyyar da ta sake gudanar da sabon zaɓen fidda gwani.

Garry, wanda ya shigar da ƙara yana ƙalubalantar zaɓen fidda gwani na baya, ya ce a shirye yake ya shiga sabon zaɓen, amma ya dage cewa bai kamata a bar Pantami ya fafata ba.

Da yake magana da wakilinmu, Garry ya ce wani kwamiti da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Ahmed Makarfi, ya jagoranta ne ya tantance ’yan takarar gwamna kafin zaɓen fidda gwanin da aka soke.

Ya yi zargin cewa an hana wasu daga cikin ’yan takarar da suka kammala tantancewa damar shiga zaɓen fidda gwanin, lamarin da ya ce shi ne ya sa aka garzaya kotu domin neman haƙƙi.

A cewarsa, daga bisani kotu ta soke zaɓen tare da umartar PDP da ta gudanar da sabon zaɓen fidda gwani na gwamna.

Garry ya ce shi da wasu ’yan takara sun shigar da ƙorafi ga shugabancin PDP da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), inda suka nemi a cire Pantami daga cikin waɗanda za su fafata a sabon zaɓen.

Ya yi hujjar cewa Pantami ya koma PDP ne bayan da jam’iyyar ta riga ta gabatar wa INEC jerin sunayen ’yan takararta na gwamna.

“Pantami ya koma PDP ne a ranar 19 ga Mayu, kuma kotu ma ta tabbatar da hakan. Saboda haka, sunansa bai cikin jerin ’yan takarar jam’iyyar da aka gabatar wa INEC ba. Bai kamata a bar shi ya shiga sabon zaɓen fidda gwani ba,” in ji Garry.

Ya yi kira ga PDP da INEC da su tabbatar da an gudanar da sabon zaɓen cikin gaskiya da adalci, tare da bin umarnin kotu.

Sai dai Garry ya ce har yanzu yana nan daram da aniyarsa ta shiga zaɓen, yana mai cewa zai fafata matuƙar jam’iyyar ta samar da yanayi na bai wa dukkan ’yan takara damar yin takara cikin adalci.

Shi ma da yake tsokaci kan sabon zaɓen, Mailantarki ya yi kira ga shugabancin PDP da ya tabbatar da an gudanar da zaɓen cikin gaskiya, adalci da kuma sahihanci.

Tsohon ɗan majalisar wakilai na Tmtarayya ya ce a shirye yake ya fafata neman tikitin jam’iyyar, inda ya buƙaci magoya bayansa da sauran ’yan PDP a faɗin jihar su kwantar da hankalinsu tare da ci gaba da kasancewa cikin haɗin kai.

Ya ce jam’iyyar na buƙatar ɗan takarar da ke da gogewar siyasa da kuma karɓuwa a tsakanin jama’a gabanin zaɓen gwamna na 2027.

Mailantarki ya buƙaci shugabancin jam’iyyar da ya bai wa dukkan ’yan takarar dama iri ɗaya, yana mai cewa adalci da gaskiya suna da muhimmanci wajen tabbatar da haɗin kan PDP.

Ya ce hukuncin kotun ya ƙara tabbatar da damuwar da ya taɓa bayyana a baya game da yadda aka gudanar da zaɓen fidda gwanin farko, wanda ya yi zargin cewa an samu wasu kura-kurai.

Ɗan takarar ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su mutunta sakamakon sabon zaɓen, tare da tabbatar da cewa an gudanar da shi bisa ƙa’idojin jam’iyya da umarnin kotu.

PDP ta sanya ranar Talata, 29 ga Satumba, domin gudanar da sabon zaɓen fidda gwani na takarar gwamnan Jihar Gombe.

By ukarofi

Leave a Reply