Hajjin 2021: Saudiyya ta tabbatar za a yi Hajji amma cikin matakai na musamman

Daga WAKILINMU

Ma’aikatar harkokin Hajji da Umura ta Ƙasar Saudiyya ta bada tabbacin cewa za a gudanar da Hajjin bana amma cikin matakan kariyar lafiya sakamakon annobar korona.

A wata sanarwar da ta fitar a Lahadi, ma’aikatar ta ce za a yi Hajjin na bana ne bayan da aka tanadi matakai na musamman game da sha’anin tsaro da kuma kariya ga lafiyar mahajjata.

“Hukumar lafiya ta Saudiyya za ta ci gaba da yin nazari a kan yanayin domin ɗaukar ƙwararan matakai don ganin cewa an kare lafiyar al’umma”, in ji sanarwar.

Ma’aikatar ta ce nan gaba kaɗan za ta bayyana irin tsare-tsare da tanade-tanaden da ta yi domin tabbatar da an yi aikin Hajjin na bana cikin lumana da kuma kwanciyar hankali.