Hajjin bana sai mazauna Saudiyya – Gwamnatin Saudiyya

Daga BASHIR ISAH

Game da hajjin bana, Ƙasar Saudiyya ta ce za a rage yawan maniyyata da adadin bai wuce mutum 60,000, kuma duka maniyyatan za su zamana mazauna ƙasar ne ban da na waje saboda annobar korona.

Saudiyya ta ba da sanarwar hakan ne a wannan Asabar ta wani kamfaninta na dilancin labarai.

Da wannan, ya tabbata cewa hajjin 2021 na mazauna Saudiyya ne kawai amma ban da sauran ƙasashen duniya.

Ko a shekarar da ta gabata mazauna Saudiyya da ba su wuce 1,000 ne aka zaɓe su suka gabatar da hajji.

Kashi biyu bisa uku na mahajjatan baƙi ne daga wajen Saudiyya, sannan kashi guda jami’an tsaro ne da ma’aikatan lafiya na Saudiyya.

Ana sa ran soma aikin hajjin na bana ne ya zuwa tsakiyar Yuli mai zuwa.