Ranar Dimukuraɗiyya: Mun cire ‘yan Nijeriya milyan 10 daga ƙangin talauci cikin shekara biyu – Buhari

Daga AISHA ASAS

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya ce gwamnatinsa ta yi nasarar cire ‘yan Nijeriya su milyan 10.5 daga ƙangin talauci a tsakanin shekaru biyu da suka gabata.

Buhari ya bayyana haka ne a jawabinsa na Ranar Dimukuraɗiyya ta bana da ya gabatar wa ‘yan Nijeriya a ranar Asabar.

Bayanan Bankin Duniya sunan Nijeriya na daga cikin ƙasashen da suke da mutane masu fama da matsanancin talauci.

Idan dai za a iya tunawa, a 2019 Buhari ya yi alƙawarin raba ‘yan Nijeriya milyan 100 da talauci a cikin shekaru goma.

Yayin jawabinsa na ran Asabar shugaban ya ce, “Duk da irin cigaban da aka samu wanda a bayyane yake, ni ne mutum na farko da zan yi amannar cewa da sauran ayyuka da dama da ya kamata a aiwatar kuma muna yin bakin ƙoƙarinmu duk da ƙarancin arzikin da ƙaruwar al’umma da muke fuskanta wajen samar da ayyuka ga al’umma.”

A cewarsa, “Cikin shekaru biyun da suka gabata mun cire mutane miliyan 10.5 daga ƙangin talauci – manoma, ƙananan ‘yan kasuwa, mata ‘yan kasuwa da sauransu.

“Na gamsu cewa za mu iya cimma ƙudurin raba mutum miliyan 100 da talauci, wannan ne ma ya samar da shirin nan na rage talauci na ƙasa. Za a ba da cikakken bayani kan shirin ba da daɗewa ba.”

Ya ce a shekara ɗaya da ta gabata ilahirin duniya an yi fama da annobar korona, lamarin da babu wanda ya yi masa cikakken shiri.

Ya ƙara da cewa shirin raba ‘yan ƙasa da talauci shi ne irinsa na farko a faɗin Afirka kuma ɗaya daga cikin mafi girma a faɗin duniya, inda sama da mutum miliyan 32.6 ke cin moriyar shirin.

Shugaban Ƙasar ya ce, “A halin da ake ciki muna da kundin sunayen matalauta da marasa galihu da aka tattaro a tsakanin ƙanan hukumomi 708, unguwanni 8,723 da ƙauyuka 86,610 kuma a tsakanin jihohi 36 haɗa da birnin Abuja.

“Shirinmu na ‘conditional cash transfer’ ya amfani mabuƙata sama da milyan 1.6 inda aka yi ta raba dubu N10,000 duk wata ga waɗanda suka ci gajiyar shirin.”