Ƙanin mahaifin Farfesa Abdalla ya kwanta dama

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Allah Ya yi wa kwaun Farfesa Abdalla Uba Adamu, Alhaji Muhammad Ɗanbala Adamu Daneji (wanda aka fi sani da Kawu Dambala) rasuwa a jiya Juma’a, 12 ga Yuni, 2021 jim kaɗan bayan Sallar Magabriba bayan gajeriyar rashin lafiya. Ya rasu yana da shekaru 83.

Shi dai marigayin ƙani ne ga Dr. Muhammad Uba Adamu Daneji, watau Kantoma, wanda Allah Ya yi wa rasuwa bara. Ya rasu ya bar matarsa, Hajiya Duduwa da ‘ya’ya shida.

Ɗaya daga cikin mutanen da marigayin ya riƙe sun haɗa da Farfesa Abdalla Uba Adamu, wanda ya yi shugabancin Buɗaɗɗiyar Jami’ar Nijeriya, watau NOUN, kuma fitaccen malami ne a Jami’ar Bayero a tsangayar aikin Jarida.

An yi jana’izarsa a gidansa da ke unguwar Daneji yau, Asabar da ƙarfe 8.30 na safiya.

Muna adduar Allah ya jiƙan sa da rahama, amin.